Batanci ga Allah: Gwamnatin Kano ta yi wa UNICEF martani kan shiga maganar Omar Farouk

Batanci ga Allah: Gwamnatin Kano ta yi wa UNICEF martani kan shiga maganar Omar Farouk

- Gwamnatin Kano ta ce laifi ne asusun UNICEF ya tsoma baki akan shari'ar jihar, kasancewar ko kasashen turai ba sa jayayya da hukuncin kotu

- A ranar 10 ga watan Satumba, wata kotun shari'a ta yankewa Farouk hukuncin shekaru 10 a gidan kaso, bayan samunsa da laifin furta kalaman batanci ga Allahu S.W.A

- Sai dai, wakilin UNICEF a Nigeria, Peter Hawkins ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta gaggauta janye wannan hukunci da aka yankewa Omar Farouk

Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Kano, Mai shari'a Musa Abdullahi Lawan ya ce laifi ne asusun UNICEF ya tsoma baki akan hukuncin da kotu ta yankewa Omar Farouk.

Mai shari'ar ya ce, bai kyauta ba, ace wai har UNICEF ta bukaci gwamnatin Kano ta sa baki a janje hukuncin daurin shekaru 10 da ake yankewa matashin, da aka kama da laifin batanci ga Allah.

Wakilin UNICEF a Nigeria, Peter Hawkins a baya bayan nan ya yi kira ga gwamnatin Nigeria da jihar Kano da su gaggauta janye wannan hukunci da aka yankewa matashin.

KARANTA WANNAN: Ma'aikata sun garkame ofishin hukumar PCC, sun hana kowa shiga

Batanci ga Allah: Gwamnatin Kano ta yi wa UNICEF martani kan shiga maganar Omar Farouk
Batanci ga Allah: Gwamnatin Kano ta yi wa UNICEF martani kan shiga maganar Omar Farouk
Asali: Twitter

Ya ce, "Yanke hukunci ga wannan yaron, mai shekaru 13, Omar Farouk, zuwa magarkama na tsawon shekaru 10 ba dai dai bane. Ya sabawa dokokin kare hakkokin yara, laifi ne hakan."

Sai dai, a martanin da ya mayarwa asusun, Antoni Janar na jihar ya ce akwai rade radin cewar wanda aka yankewa hukuncin shekarunsa 13, amma kotu ta tabbatar shekarunsa 17.

"Ga UNICEF ta ce wai gwamnatin jiha ta sa baki a maganar, to ta sani babu wata kasa da gwamnati ke tsoma baki a hukuncin da kotu ta yanke.

"Ma damar kotun shari'a ta yanke hukunci, to abu na gaba da za a iya yi idan an samu matsala shine dayan bangaren ya daukaka kara," a cewar sa.

"Kuma a irin wannan misalin, Omar Farouq na da 'yancin daukaka kara, har zuwa kotun koli, kuma idan har yaro ne, kotu za ta binciko hakan idan ya daukaka kara.

"Don haka wai batun UNICEF ta ce gwamnatin jihar Kano ta shiga cikin maganar, wannan kuskure ne," a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Shugaban kasa Buhari ya marabci shugaban kasar Burkina Faso (Hotuna)

Ya ce, "Babu wata kasar Turai ko Amurka, da ke sa baki idan kotu ta yanke hukunci. Kuma iya sani na shine, yaron ya daukaka kara, don haka a jira aka hukuncin kotun daukaka karar."

Idan ba a manta ba, a ranar 10 ga watan Satumba, wata kotun shari'a ta yankewa Farouk hukuncin shekaru 10 a gidan gyara hali, bayan samunsa da laifin furta kalaman batanci ga Allahu S.W.A a wata muhawara da suka yi a ranar 4 ga watan Maris.

Mai shari'ar kotun, Khadi Muhammad Ali-Kani, a hukuncin da ya yanke, ya ce laifin ya sabawa dokar Musulunci, kuma ya yanke masa shekaru 10 a gidan gyara hali.

A karkashin sashe na 382 (b) na dokokin laifuka da hukunci na jihar Kano da aka sabunta a 2000, mai shari'ar ya yanke hukuncin, amma ya bashi damar daukaka kara a cikin kwanaki 30.

A wani labarin, Ayyukan shelkwatar hukumar karbar korafe korafen al'umma da ke Abuja, ya samu tsaiko, sakamakon kulle kofofin ginin da fusatattun ma'aikatan hukumar suka yi.

Masu zanga zangar, a ranar Laraba, sun kulle babbar kofar shiga cikin hukumar, inda suka hana kowa shiga, a zanga zangar da suke soma yi ta neman hakkokinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel