Babbar magana: Ma'aikata sun garkame ofishin hukumar PCC, sun hana kowa shiga

Babbar magana: Ma'aikata sun garkame ofishin hukumar PCC, sun hana kowa shiga

- Fusatattun ma'aikatan hukumar karbar korafe korafen al'umma, PCC sun garkame kofar ginin hukumar, sun hana kowa shiga

- Masu zanga zangar, sun ce ba zasu bude kofar ginin ba har sai hukumar ta biyasu hakkokinsu na watanni 17 da ake so a cinye masu

- A cewar ma'aikatan, za su shiga yajin aiki ma damar kulle kofar shiga ginin bai haifar masu da d'a mai ido ba

Ayyukan shelkwatar hukumar karbar korafe korafen al'umma da ke Abuja, ya samu tsaiko, sakamakon kulle kofofin ginin da fusatattun ma'aikatan hukumar suka yi.

Masu zanga zangar, a ranar Laraba, sun kulle babbar kofar shiga cikin hukumar, inda suka hana kowa shiga, a zanga zangar da suke soma yi ta neman hakkokinsu.

Kulle kofar ginin ya jefa hukumar cikin rudani, yayin da ma'aikata karkashin kungiyar JUPCC, ke zanga zanga na rashin biyansu albashi mafi karanci da hakkokinsu na watanni 17.

KARANTA WANNAN: Shugaban kasa Buhari ya marabci shugaban kasar Burkina Faso (Hotuna)

Babbar magana: Ma'aikata sun garkame ofishin hukumar PCC, sun hana kowa shiga
Babbar magana: Ma'aikata sun garkame ofishin hukumar PCC, sun hana kowa shiga
Asali: Twitter

Suna dauke da kwalaye masu rubutuka daban daban, kamar 'albashi mafi karanci hakkinmu ne, a biyamu yanzu', 'Albashin ma'aikata doka ce ba alfarma ba.'

'Mun gaji da rashin biyanmu hakkokinmu', da kuma 'Shugaba Buhari, kada ka kashe masu karbar korafe korafen jama'a' da dai sauran sakonni.

Kungiyar JUPCC ta hada da kungiyar ma'aikatan dokar hukumar PSAN, kungiyar manyan ma'aikatan gwamnati ASCSN da kuma kungiyar ma'aikata NCSU.

KARANTA WANNAN: Nigeria ta samu babban ci gaba a kwallon duniya, ita ce ta 29 - FIFA

A cewar ma'aikatan, za su shiga yajin aiki ma damar kulle kofar shiga ginin bai haifar masu da d'a mai ido ba.

A yayin da suke zargin gwamnati na wofantar da ma'aikatar, ma'aikatan sun ce za su ci gaba da mamaye harabar ma'aikatar, har sai hukumar ta biyasu kudaden su.

Mataimakin shugaban kungiyar NSCU (A matakin kasa), Isa Degri, ya shaidawa manema labarai cewa masu zanga zanga zasu ci gaba da garkame ginin har sai an biyasu hakkokinsu.

Ya ce, "Ba bu yadda za a yi su ci gaba da aiki alhalin ba a biyansu albashinsu, kusan watanni 17 kenan ba a biyasu hakkokinsu ba. Za mu ci gaba da mamaye ginin har sai an biya kudaden.

"Babban abunda ke damunmu shine har yanzu ba a kaddamar da albashi mafi karanci ga ma'aikatanmu ba. Watanni 17 ke nan ba su biya ba; balle ayi maganar kudaden hutu."

A wani labarin, Laolu Akande ya kare gwamnatin tarayya biyo bayan cece kuce da mamaye kasar sakamakon karin kudin wutar lantarki, yana mai cewa komai zai koma dai dai nan ba da jimawa ba.

Akande, hadimi na musamman ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ta fuskar watsa labarai, ya yi amanna da cewa karin kudin zai amfani 'yan Nigerian.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel