Babbar magana: Ƴan bindiga sun kai wa ƴan sanda hari a Sokoto 'sun kashe DPO'

Babbar magana: Ƴan bindiga sun kai wa ƴan sanda hari a Sokoto 'sun kashe DPO'

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari garin Gidan Madi, karamar hukumar Tangaza, da ke a jihar Sokoto

- A yayin kai harin, 'yan bindigar sun kashe DPO na garin, tare da yin awon gaba da wasu mata da ba asan adadin su ba

- Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kai harin, sai dai ba ta yi wani karin haske kan batun kashe DPO din ba

Rahotanni daga BBC, na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan bindiga ne suka kai hari garin Gidan Madi, karamar hukumar Tangaza, da ke a jihar Sokoto.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, yan bindigar sun farmaki ofishin rundunar 'yan sandan ne da tsakiyar dare, inda har suka samu damar kashe DPO na garin.

Mazauna garin sun tabbatar da faruwar lamarin, a cewar BBC.

Wani ganau da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa ya ji karar harbe harbe a tsakiyar dare, lamarin da ya tilastasu tashi daga barci.

KARANTA WANNAN: Karin kuɗin wutar lantarki: Da sannu ƴan Nigeria za su gane amfanin hakan - FG

Babbar magana: Ƴan bindiga sun kai wa ƴan sanda hari a Sokoto 'sun kashe DPO'
Babbar magana: Ƴan bindiga sun kai wa ƴan sanda hari a Sokoto 'sun kashe DPO'
Source: Twitter

Duk da cewa bai yi karin haske kan kashe DPO da yan bindigar suka yi ba, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Sokoto, ASP Muhammad Sadiq, ya tabbatar da kai harin.

Bayan 'yan bindigar sun kashe DPO, sun kuma shiga cikin garin Gidan Madi, inda suka yi awon gaba da wasu mata, kamar yadda mazauna garin suka tabbatar.

Haka zalika, rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun yi awon gaba da makamai, musamman bindiga kirar AK47.

KARANTA WANNAN: Yakin neman zabe: Atiku ya mayar wa Tinubu martani a kan zaben Edo

"Jami'an rundunar 'yan sandan suna zaune a harabar ofishin rundunar a lokacin da yan bindigar suka far masu, har suka samu damar kashe DPO," cewar mazaunin garin.

Ba tun yanzu jihar Sokoto ke ci gaba da fuskantar hare haren yan bindiga ba, inda ko da a baya bayan nan an kai hari garin Tangaza, inda suka yi awon gaba da amarya da mai jego.

Ba iya jihar Sokoto kadai ba, jihohin shiyyar Arewa maso Yamma, musamman Katsina, Zamfara, wani yanki na Kaduna, suna fama da hare haren yan bindiga.

Wannan kuwa ya na ci gaba da faruwa, duk da cewa gwamnatin tarayya tana ikirarin cewa ta dauki matakan kawo karshen kai hare hare a fadin kasar.

Dubunnan mutane ne suka rasa muhallansu, wasun su a yanzu suna zama a sansanonin gudun hijira, yayin da aka yi asarar rayuka da dukiya mai yawa.

A wani labarin, Hukumar kula da tashoshin layin dogo ta Nigeria (NRC) ta karyata rahoton cewa yan bindiga sun kaiwa jirgin Abuja-Kaduna K14 hari a tsakanin garin Asham da Kubwa a ranar Litinin.

Shugaban hukumar NRC, Fidet Okhiria, wanda ya karyata labarin a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ya ce labaran kanzon kurege ne kawai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel