Zargin luwadi: Kotu ta bukaci a adana mata makaho a gidan yari

Zargin luwadi: Kotu ta bukaci a adana mata makaho a gidan yari

- Wata kotun majistare da ke zama a Dutse a jihar Jigawa ta bukaci a adana mata wani makaho a gidan gyaran hali

- Alkalin kotun mai suna Akilu Isma'il, ya ce a adana masa makaho Muhammad Abdul har zuwa ranar 5 ga watan Oktoba

- Ana zarginsa da jan dan jagoransa zuwa wani daji da ke bayan kotu, inda ya yi yunkurin luwadi da shi

Wata kotun majistare da ke garin Dutse a jihar Jigawa a ranar Laraba, ta bada umarnin adana mata wani makaho mai shekaru 60 mai suna Muhammad Abdul.

Ana zarginsa da yunkurin yin luwadi da dan jagorarsa, lamarin da yasa aka bukaci adanasa a gidan gyaran hali.

Alkalin kotun majistaren mai suna Akilu Isma'il, wanda ya umarci a adana masa Abdul a gidan gyaran halin, ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Oktoba.

'Yan sandan sun gurfanar da Abdul, wanda ke zama a karamar hukumar Guru ta jihar Yobe, sakamakon zarginsa da yunkurin aikata mugun aikin.

Tun farko, babban lauyan mai gurfanarwa, Kabiru Warwade, ya sanar da kotun cewa Abdul ya aikata laifin a ranar 8 ga watan Satumba wurin karfe 10 na safe a kwatas din Garko da ke karamar hukumar Hadejia.

Warwade ya ce Abdul ya ja yaron zuwa dajin da ke bayan kotun Shari'a da ke Hadejia, kuma ya yi yunkurin luwadi da shi.

Dan sanda mai gabatar da karar ya ce, hakan ya ci karoo da tanadin sashi na 95 na dokokin Penal Code, The Nation ta wallafa.

KU KARANTA: Za a fara rataye masu yiwa mata fyade ko kuma a basu guba a kasar Pakistan

Zargin luwadi: Kotu ta bukaci a adana mata makaho a gidan yari
Zargin luwadi: Kotu ta bukaci a adana mata makaho a gidan yari. Hoto daga The Nation
Source: Getty Images

KU KARANTA: Najeriya ce kasar da tafi kowacce kasar bakar fata cigaba a duniya - Shugaba Buhari

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kwara ta gurfanar da wani malamin makaranta a gaban kotu bayan da aka zargesa da yunkurin lalata da dalibarsa mai shekaru bakwai a duniya.

An gano cewa, malamin mai suna Akorede Hammed, ya kai yarinyar cikin bandakin makaranta inda ya yi mata tsirara tare da fara wasa da gabanta, kamar yadda rahoton farko na 'yan sanda ya bayyana.

Bayanin yadda lamarin ya faru yana kunshe a wasikar mahaifin yarinyar wanda ya rubuta a ofishin 'yan sandan yankin da ke Ilorin, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

A wasikar, ya sanar da cewa Hammed ya shiga da yarinyar bandaki, ya garkame kofa sannan ya fara tattabata. Daga bisani malamin ya bude kofar tare da sakin yarinyar bayan da ta ki amincewa da muguwar bukatarsa.

Binciken 'yan sanda ya nuna cewa, wanda ake zargin shine malamin yarinyar, kuma ya tsere daga makarantar inda ya boye tun bayan aukuwar lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel