Tarihi ya kafu, jirgin kasa ya tashi daga Legas zuwa Ibadan (Bidiyo)

Tarihi ya kafu, jirgin kasa ya tashi daga Legas zuwa Ibadan (Bidiyo)

- Akwai yuwuwar titin dogo na Legas zuwa Ibadan zai iya fara aiki a kowanne lokaci saboda wani jirgin kasa ya bar tashar Ebute Metta zuwa Ibadan a ranar Laraba

- A cikin jirgin kasan akwai hadimi na musamman ga shugaba Buhari, Tolu Ogunlesi, wanda ya ce ana aikin tashar Mobolaji

- Tolu ya jinjina yadda jirgin kasan zai zamo wata hanya ta rage cunkoson titunan Legass kuma babban hanyar sufuri ga jama'a

Akwai yuwuwar fara aikin titin jirgin kasa wanda ya fara daga Legas zuwa Ibadan a koda yaushe daga yanzu.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Tolu Ogunlesi, ya wallafa wani bidiyon jirgin kasa wanda yake barin Ebute Metta a Legas zuwa Ibadan.

'Yan jihar Legas tare da sauran masu kai da kawowa daga Ibadan, kwanan nan za su yi bankwana da matsalar cunkoson kan titi da ta addabi birnin.

Wani bidiyo ya bayyana inda ake aikin tashar jirgin kasan. A bidiyon, an ga jirgin kasan yana tafiya ba tare da wani shamaki ba.

Mutane da yawa sun yi tsokaci a kan wannan cigaban tare da bayyana cewa hakan zai iya shawo kan matsalar wurin kwana a jihar Legas.

KU KARANTA: UK tana barazanar kwace kadarorin 'yan siyasar da za su yi magudi a zabukan Edo da Ondo

Tarihi ya kafu, jirgin kasa ya tashi daga Legas zuwa Ibadan (Bidiyo)
Tarihi ya kafu, jirgin kasa ya tashi daga Legas zuwa Ibadan (Bidiyo). Hoto daga Tolu Ogunlesi
Source: UGC

KU KARANTA: Idan har Buhari bai canja takunsa ba nan da 2023 Najeriya za ta zama ba tamu ba - Fani Kayode

Ga bidiyo da tsokacin jama'a:

A wani labari na daban, a yayin da Najeriya ke shirin bikin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Najeriya a matsayin kasar bakar fata da suka fi kowa samun cigaba a duniya da kuma tattalin arziki.

Shugaban kasar ya bayyana hakane a yau 16 ga watan Satumba a babban birnin tarayya Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina, ya fitar, shugaban kasar yana cewa: "A yau mun zaya akan abubuwa na tarihi, inda muka fara gabatar da bukukuwa na murnar cikar Najeriya.

"Murnar cika shekaru 60 da samun 'yancin kai na da muhimmanci, amma cutar COVID-19, wacce ta addabi kowacce kasa ta duniya ta sanya komai ya canja, hakan ya sanya muka gabatar da bikin ba kamar yadda aka saba gabatarwa ba.

"Najeriya kasa dake da yawan mutane sama da miliyan 200, da suke da tsantsar basira, muna da matukar muhimmanci a idon duniya. Waannan a gare ni wani abun alfahari ne. Duk inda ka shiga a duniya, 'yan Najeriya ne kan gaba, ko a bangaren ilimi, bangaren kasuwanci, bangaren cigaba, bangaren nishadi, bangaren al'ada da sauransu.

"Haka kuma hoton gwal dake jikin taswirar mu ta nuna cewa muna da matukar muhimmanci, 'yan Najeriya na da matukar muhimmanci a idon duniya. Duka wadannan abubuwa sune suka saka muka zama kasar da tafi kowacce kasar bakar fata cigaba a duniya, sannan kuma ta zama kasar da tafi kowacce karfin tattalin arziki a Afrika. Wannan babban abin alfahari ne ga mutanen da suke aiki sau da kafa domin cigaban kasar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel