Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS a kasar Ghana

Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS a kasar Ghana

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a taron kungiyar ECOWAS da za a gudanar a Ghana

- Rahotanni sun bayyana cewa taron zai mayar da hankali wajen kawo karshen rikicin siyasa da ya mamaye kasar Mali

- Haka zalika, mataimakin shugaban kasar, zai gana da yan Nigeria mazauna Ghana

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Talata ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a taron kungiyar kasashe masu tattalin arziki na Yammacin Afrika (ECOWAS) a Ghana.

Taron da ake gudanar da shi a Accra, babban birnin kasar, na daga cikin yunkurin shuwagabannin kasashen na kawo karshen rikicin kasar Mali.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda za ta tura jami'ai 31,000 zaben Edo, ta bayyana dalili

A cikin wata sanarwa a ranar Talata daga Laolu Akande, hadimin Osinbajo a fuskar watsa labarai, ya ce mataimakin shugaban kasar zai kuma gana da 'yan Nigeria mazauna Ghana.

A watan Agusta, yan Nigeria da ke kasuwanci a Ghana sun koka kan yadda hukumomin Ghana suka rufe shagunansu, biyo bayan umurnin da gwamnatin kasar ta bayar.

DUBA WANNAN: Hanyar Kaduna: Rundunar NPF da hukumar NRC sun yi baki biyu a kan kai wa jirgin kasa hari

Wannan ya faru watanni biyu bayan da aka rusa wani ginin Nigeria a kasar Ghana.

Ga hotunan taron.

Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS a Ghana
Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS a Ghana
Asali: Twitter

Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron ECOWAS
Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron ECOWAS
Asali: Twitter

Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS
Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS
Asali: Twitter

Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS a Ghana
Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS a Ghana
Asali: Twitter

A wani labarin, Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya bayyana cewa za a tura jami'an 'yan sanda 31,000 zuwa jihar Edo domin kare ma'aikatan zabe, kayan zabe, da kuma tabbatar da doka.

Tuni hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, a matsayin ranar zaben kujerar gwamnan jihar Edo.

"Mun tura jami'an 'yan sanda ma su yawa domin takawa duk wasu batagarin 'yan siyasa burki.

"Duk wanda ya sabawa doka ko kuma ya yi kokarin tayar da fitina za a gurfanar da shi.

"Rundunar 'yan sanda za ta bayar da kariya ga wadanda su ka fita domin kada kuri'a cikin mutunci," kamar yadda IGP Adamu ya bayyana yayin taro da masu ruwa da tsaki a Benin ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel