Hanyar Kaduna: Rundunar NPF da hukumar NRC sun yi baki biyu a kan kai wa jirgin kasa hari

Hanyar Kaduna: Rundunar NPF da hukumar NRC sun yi baki biyu a kan kai wa jirgin kasa hari

- Hukumar NRC ta karyata labaran da ke yawo a kafofin sadarwa na cewar an kaiwa jirgin kasa mai lamba K14 hari a hanyar Abuja-Kaduna

- Haka zalika, rundunar 'yan sanda itama ta karyata cewa 'yan bindiga ne suka kai hari, tana kan binciken lamarin

- Sai dai, gaba daya bangarorin biyu, hukumar NRC da rundunar NPF sun tabbatar da cewa bata gari ne suka wurga duwatsu a jirgin

Hukumar kula da tashoshin layin dogo ta Nigeria (NRC) ta karyata rahoton cewa yan bindiga sun kaiwa jirgin Abuja-Kaduna K14 hari a tsakanin garin Asham da Kubwa a ranar Litinin.

Shugaban hukumar NRC, Fidet Okhiria, wanda ya karyata labarin a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ya ce labaran kanzon kurege ne kawai.

A cewar sa, akan samu bata gari a mafi akasarin lokuta, wadanda ke wurga duwatsu idan jirgin na tafiya, a hanyar Abuja-Kaduna.

KARANTA WANNAN: Zaben 2020: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda bai cika ba a Amurka

Hanyar Kaduna: Rundunar NPF da hukumar NRC sun yi baki biyu a kan kai wa jirgin kasa hari
Hanyar Kaduna: Rundunar NPF da hukumar NRC sun yi baki biyu a kan kai wa jirgin kasa hari
Asali: UGC

"Babu wasu 'yan bindigar da suka kaiwa jirgin harin; labarin kanzon kurege ne, ai da sun ga ruwan harsasai a cikin jirgin.

"Wasu bata gari ne kawai wadanda ke jifar jirgin da duwatsu, kuma saboda yan sanda sun cafke wani daga cikin su, shi ya sa suke jifar jirgi idan yazo wucewa da daddare don nuna bacin ransu.

"Sai dai, hukumar NRC, ta tattauna da hukumomin tsaro domin dakile faruwar irin hakan a nan gaba, su zasu fi mu sanin mafi dacewar hanyar dakile irin hakan," a cewar Okhiria.

Ya kuma bukaci daukacin al'umma da ke amfani da jiragen kasan, da su kwantar da hankulansu, da basu tabbacin cewa ministan zirga zirga da hukumar NRC za ta kare rayuka da dukiyoyinsu.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun kaiwa jami'an FRSC hari, sun kashe 2, sun sace 10

A hannu daya, shugaban ofishin kula da layin dogon Abuja-Kaduna, Paschal Nnorli, ya tabbatar da cewa jirgin ya isa tashar Idu a kan lokaci a ranar Litinin, ya karyata kaiwa jirgin hari.

"Ma'aikata da jami'an rundunar 'yan sanda da ke tsaron jirgin sun bi bayan bata garin, sai dai jirgin ya ci gaba da jigilarsa, bai tsaya ko ina ba sai tashar Idu," a cewar sa.

A wani labarin, Hukumar yan sandan Najeriya ta saki jawabi akan harin da aka kai wa fasinjojin jirgin kasa tsakanin garin Asham da Kubwa dake hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kakakin hukumar na jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN a hirar wayar tarho cewa jirgin ya isa Kaduna lafiya.

Ya tabbatar da labarin cewa wasu matasa ne suka jefi jirgin da duwatsu a kauyen Rijana, cikin Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel