Rundunar 'yan sanda za ta tura jami'ai 31,000 zaben Edo, ta bayyana dalili

Rundunar 'yan sanda za ta tura jami'ai 31,000 zaben Edo, ta bayyana dalili

- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa za ta tura jami'anta 31,000 a jihar Edo, domin kare ma'aikatan zabe da kayan zabe

- Daga cikin dalilan tura jami'an, a cewar Sifeta Janar na rundunar, Mohammed Adamu, akwai tabbatar da doka da yin zaben cikin luma

- Kazalika, IGP Adamu ya bukaci jami'an da ke aiki da manyan mutane da su kauracewa raka iyayen gidansu zuwa wurin kada kuri'a a ranar zabe

Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya bayyana cewa za a tura jami'an 'yan sanda 31,000 zuwa jihar Edo domin kare ma'aikatan zabe, kayan zabe, da kuma tabbatar da doka.

Tuni hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, a matsayin ranar zaben kujerar gwamnan jihar Edo.

"Mun tura jami'an 'yan sanda ma su yawa domin takawa duk wasu batagarin 'yan siyasa burki.

KARANTA WANNAN: Hanyar Kaduna: Rundunar NPF da hukumar NRC sun yi baki biyu a kan kai wa jirgin kasa hari

Rundunar 'yan sanda za ta tura jami'ai 31,000 zaben Edo, ta bayyana dalili
Rundunar 'yan sanda za ta tura jami'ai 31,000 zaben Edo, ta bayyana dalili
Source: Depositphotos

"Duk wanda ya sabawa doka ko kuma ya yi kokarin tayar da fitina za a gurfanar da shi.

"Rundunar 'yan sanda za ta bayar da kariya ga wadanda su ka fita domin kada kuri'a cikin mutunci," kamar yadda IGP Adamu ya bayyana yayin taro da masu ruwa da tsaki a Benin ranar Litinin.

A Ranar Juma'a ne IGP Adamu ya tura wasu manyan jami'an 'yan sanda zuwa jihar Edo domin su saka ido a kan zaben kujerar gwamna mai zuwa.

Babban mataimakin sifeton rundunar 'yan sanda (DIG), Adeleye Olusola Oyabade, ne jagoran tawagar manyan jami'an da IGP Adamu ya tura.

KARANTA WANNAN: Zaben 2020: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda bai cika ba a Amurka

DCP Frank Mba, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, ya ce; AIG Hosea Hassan zai kasance mataimaki ga DIG Oyabade.

A cikin wata sanarwa da DCP Mba ya fitar yau, Juma'a, rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa aikin manyan jami'an shine tabbatar da tsaro a jihar Edo.

Rundunar 'yan sanda ta ce ta dorawa tawagar alhakin tabbatar da ganin cewa an gudanar da zaben jihar Edo cikin lumana.

"Sauran manyan jami'an 'yan sanda da ke cikin tawagar sun hada da CP Garba Baba Umar, CP Habu Sani, CP Buba Sanusi da CP Akeera M. Yonous.

"Sauran hudun sune; CP Omololu S. Bishi, CP Abutu Yaro, CP Philip Aliyu Ogbadu da CP Olokade T. Olawale," a cewar sanarwar mai dauke da sa hannun DCP Mba.

Sanarwar ta kara da cewa za a bawa kowanne daya daga cikin manyan jami'an bangaren aikin da zai mayar da hankali a kansa.

Kazalika, IGP Adamu ya bukaci jami'an 'yan sanda da ke aiki da manyan mutane su kauracewa raka iyayen gidansu zuwa wurin kada kuri'a a ranar zabe.

A wani labarin, Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton cewa yan bindiga ne sun kaiwa jami'an hukumar FRSC hali a ranar Linitin, sun kashe 2 tare da yin garkuwa da wasu 10.

Jami'in hukumar na tafiya a motoci guda biyu, su 26, sun fito daga sansanonin hukumar da ke Sokoto da Kebbi, inda suka karbi wani hoto a makarantar FRSC, Udi, birnin Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel