Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kaiwa jami'an FRSC hari, sun kashe 2, sun sace 10

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kaiwa jami'an FRSC hari, sun kashe 2, sun sace 10

- Yan bindiga sun farmaki jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, inda suka kashe 2 tare da yin garkuwa da guda 10

- An ruwaito cewa, an kai masu harin ne a sha tale talen Udege, da ke kan hanyar Mararaban-Udege, jihar Nasawara a ranar Litinin

- Jami'an sun fito daga sansanonin hukumar da ke Sokoto da Kebbi, inda suka karbi wani hoto a makarantar FRSC, Udi, birnin Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton cewa yan bindiga ne sun kaiwa jami'an hukumar FRSC hali a ranar Linitin, sun kashe 2 tare da yin garkuwa da wasu 10.

Jami'in hukumar na tafiya a motoci guda biyu, su 26, sun fito daga sansanonin hukumar da ke Sokoto da Kebbi, inda suka karbi wani hoto a makarantar FRSC, Udi, birnin Abuja.

Kakakin hukumar kiyaye titunan, Bisi Kazeem a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, jami'an na kan hanyarsu ne yan bindigar suka kai masu harin.

KARANTA WANNAN: Mun gaji da zama a Arewa, za mu koma inda muka fito - Kungiyar Yarabawa

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kaiwa jami'an FRSC hari, sun kashe 2, sun sace 10

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kaiwa jami'an FRSC hari, sun kashe 2, sun sace 10
Source: Twitter

An ruwaito cewa, an kai masu harin ne a sha tale talen Udege, da ke kan hanyar Mararaban-Udege, jihar Nasawara, da misalin karfe 8 na safiya.

Mr Kazeem ya ce daya daga cikin jami'an ya mutu nan take a cikin motar, yayin da wani jami'in ya mutu bayan an kai shi asibiti tare da wasu guda hudu da suka jikkata.

Jami'ai takwas sun tsira da rayukansu ba tare da ko kwarzane ba, yayin da ake zargin yan bindigar sun yi garkuwa da jami'ai goma, a cewar kakakin hukumar.

KARANTA WANNAN: COVID-19: Matakin da gwamnatin Saudiya ta dauka kan rufe iyakoki da sufurin jiragen sama

Mr Kazeem ya ce tuni shugaban rundunar, CP Boboye Oyeyemi, ya sanar da lamarin ga sauran hukumomin tsaro, don ceto jami'an da kuma cafke yan bindigar.

Ya yi nuni da cewa shugaban rundunar ya yi kira ga dukkanin jami'an hukumar da su kwantar da hankulansu, kada wannan lamarin ya karyar masu da guiwa.

Ya bayar da tabbacin cewa rundunar za ta yi aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro domin gano yan bindigar tare da yanke masu hukunci, a hannu daya kuma su ceto jami'an da aka sace.

A wani labarin, Rundunar 'yan sanda ta fara bincike kan wani bidiyo da ya karade yanar gizo da ke nuna wani mutumi sanye da kakin rundunar yana shan shisha.

Rundunar a shafinta na Twitter, a ranar Lahadi ta bayyana cewa ta mika bidiyon ga sashen kwararru don gano gaskiyar bidiyon, da kuma sanin mutumin.

A cewar rundunar, gano gaskiyar bidiyon da sanin mutumin, zai tabbatar da cewa ko da gaske jami'in rundunar ne, ko sojan gona, ko kuma dai wani sashe ne na wasan kwaikwayo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel