Mun gaji da zama a Arewa, za mu koma inda muka fito - Kungiyar Yarabawa

Mun gaji da zama a Arewa, za mu koma inda muka fito - Kungiyar Yarabawa

- Al'ummar Yarabawa mazauna jihar Kogi, sun bayyana cewa lokaci ya yi da za su tattara su koma shiyyarsu ta asali, Kudu maso Yamma

- Kungiyar Yarabawan Okun, ta yi nuni da cewa, da ma sun baro mahaifarsu tare da zama a Arewa don dogaro da kai da kuma bunkasa tattalin arziki

- Kungiyar, ta aikawa majalisar tarayya bukatar sabunta dokar da ta kafa kungiyarsu, da kuma yi masu matsugunni a shiyyarsu ta asali

Kungiyar Yarabawa (Okun) mazauna jihar Kogi, sun ce suna da bukatar tattara ya nasu-ya nasu su bar shiyyar Arewa, bayan shafe tsawon shekaru suna rayuwa a ciki.

Sun bayyana cewa a baya, sun zabi barin 'yan uwansu da mahaifarsu a jihohin Ondo, Ekiti da Kwara, saboda dogaro da kai, yanzu kuma akwai bukatar su koma cikin 'yan uwansu.

Sun yi bayanin hakan ne a karkashin kungiyar OLA, a ranar Lahadi, bayan ganawarsu da Aiyetoro-Gbede, a karamar hukumar Ijumu, jihar Kogi.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kaduna ta sanar da adadin talakawan da suke rayuwa a jihar

Mun gaji da zama a Arewa, za mu koma inda muka fito - Kungiyar Yarabawa
Mun gaji da zama a Arewa, za mu koma inda muka fito - Kungiyar Yarabawa
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar, Chief Emmanuel Otitoju, wanda ya ce kungiyar ta yi nazarin abubuwan da ke faruwa a kasar, ya ce sun aikawa majalisar dokoki ta tarayya sakon bukatarsu.

A cewarsa, tuni da kungiyarsu ke da kundin tsare tsare wanda majalisar dokoki ta tarayyar ta sawa hannu, a yanzu kuma suke son a sabunta dokar, don kare ire iren kungiyoyinsu.

"Mun yi nazari sosai tare da sahalewar kundin tsarin bunkasa al'ummar Yarabawa (ODA) da aka aikawa majalisar dokoki ta tarayya domin yin nazari da kuma sabuntawa.

"Kuma, mun cimma matsaya kamar haka: cewar barin 'yan uwanmu da mahaifarmu na Kudu maso Yamma ya faru saboda neman ci gaba, wanda muka samu shekaru masu yawa.

KARANTA WANNAN: COVID-19: Matakin da gwamnati Saudiya ta dauka kan rufe iyakoki da sufurin jiragen sama

Don haka, a yanzu, muna da bukatar a sabunta dokokin da ke dauke da tsare tsaren rayuwarmu, za mu koma mahaifarmu, za mu koma inda muka fito, Kudu maso Yammacin Nigeria."

A wani labarin; Shugabar shirye shiryen bunkasa rayuwa ta jihar Kaduna, Saude Amina Ayotebi, ta bayyana cewa, annobar COVID-19 ta nunawa duniya cewa kusan kowa na da raunin tattalin arziki.

A zantawarta da jaridar Daily Trust, Saude Atoyebi, ta yi karin haske kan yadda 'yan jihar za su iya cin moriyar shirye shiryen jin kai, don bunkasa rayuwarsu.

Bayan shafe watanni ana tattaunawa tsakanin ma'aikatu, sashe sashe da kuma hukumomin da ke kula da ayyukan jin kai, jihar Kaduna ta kaddamar da dokar kariya ta bunkasa rayuwar jama'a.

Ta bayyana cewa, gwamna Nasir Ahmad Elrufai, ya dukufa wajen ganin, ya tsamo talakawa daga cikin mawuyacin hali, tare da daga darajar rayuwarsu zuwa mawadata.

Saude Ayotebi ta ce mafi akasarin shirye shiryen bunkasa rayuwa na jihar sun shafi kananan yara, mata, marasa lafiya, masu nakasa, tsofaffi da kuma ma'aikatan da suka jikkata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel