Gwamnatin Kaduna ta sanar da adadin talakawan da suke rayuwa a jihar

Gwamnatin Kaduna ta sanar da adadin talakawan da suke rayuwa a jihar

- Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa kalla mutane 825,805 ne ke rayuwa cikin talauci a jihar, wadanda suke bukatar agaji

- Gwamnatin jihar ta kuma yi nuni da cewa, annobar COVID-19 ta nunawa duniya cewa kusan kowa yana da rauni a bangaren tattalin arziki

- Sai dai, gwamnatin ta ce, ta bullo da shirye shirye, domin tallafawa rayuwar talakawan jihar, da kuma tsamo su daga kangin talauci

Shugabar shirye shiryen bunkasa rayuwa ta jihar Kaduna, Saude Amina Ayotebi, ta bayyana cewa, annobar COVID-19 ta nunawa duniya cewa kusan kowa na da raunin tattalin arziki.

A zantawarta da jaridar Daily Trust, Saude Atoyebi, ta yi karin haske kan yadda 'yan jihar za su iya cin moriyar shirye shiryen jin kai, don bunkasa rayuwarsu.

A cewar ta, bayan shafe watanni ana tattaunawa tsakanin ma'aikatu, sashe sashe da kuma hukumomin da ke kula da ayyukan jin kai, jihar Kaduna ta kaddamar da dokar kariya ta bunkasa rayuwar jama'a.

KARANTA WANNAN: Rundunar yan sanda ta fara farautar jami'inta da aka nuna yana shan shisha

Gwamnan Kaduna Nasir Elrufai
Gwamnan Kaduna Nasir Elrufai
Asali: Twitter

Ta bayyana cewa, gwamna Nasir Ahmad Elrufai, ya dukufa wajen ganin, ya tsamo talakawa daga cikin mawuyacin hali, tare da daga darajar rayuwarsu zuwa mawadata.

Saude Ayotebi ta ce mafi akasarin shirye shiryen bunkasa rayuwa na jihar sun shafi kananan yara, mata, marasa lafiya, masu nakasa, tsofaffi da kuma ma'aikatan da suka jikkata.

"A cikin wannan tsari, gwamnati ta mayar da hankali wajen ganin ta biya hakkokin fansho, inshorar lafiya, giratuti da kuma tallafawa marasa aikin yi.

"A halin yanzu, jihar Kaduna na da gidaje 216,398, da kuma mutane 825,805 a cikinsu. Wadannan sune adadin mutanen da alkaluma suka nuna talakawa ne, masu neman agaji.

"Kuma a halin yanzu, mutane 30,000 ne ke cin gajiyar tallafin N5,000 na kowanne wata. Sannan an yiwa mutane 4,000 rejistar inshorar lafiya," a cewar shugabar shirin tallafawa gajiyayyun.

Saude Amina Ayotebi ta kuma bayyana yunkurin gwamnatin Kaduna na samar da wani shiri, da zai yi duba ga matsalolin talakawan, don basu mafitar da ta dace da su.

Ta ce daga cikin amfanin shirin tallafawa talakawa da N5,000 a kowanne wata, akwai rage talauci, bunkasa rayuwa, rage aikata laifuka saboda talauci da sauransu.

"Kafin mu ba ka kudi, sai jami'ai sun koyar da kai sana'o'in da za ka juya wadannan kudaden, hakan zai taimaka wajen farfado da kasuwanci da tattalin arziki.

"Akalla kungiyoyi 500 sun amfana da tallafin kasuwanci, wadanda suka kware a bangaren noma, da kuma samar da manja. Kuma sun samu ribar sama da N12m, rayuwarsu ta canja a yanzu."

A wani labarin, Rundunar 'yan sanda ta fara bincike kan wani bidiyo da ya karade yanar gizo da ke nuna wani mutumi sanye da kakin rundunar yana shan shisha.

Rundunar a shafinta na Twitter, a ranar Lahadi ta bayyana cewa ta mika bidiyon ga sashen kwararru don gano gaskiyar bidiyon, da kuma sanin mutumin.

A cewar rundunar, gano gaskiyar bidiyon da sanin mutumin, zai tabbatar da cewa ko da gaske jami'in rundunar ne, ko sojan gona, ko kuma dai wani sashe ne na wasan kwaikwayo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel