Bidiyo: Rundunar yan sanda ta fara farautar jami'inta da aka nuna yana shan shisha

Bidiyo: Rundunar yan sanda ta fara farautar jami'inta da aka nuna yana shan shisha

- Rundunar 'yan sanda ta fara bincike kan wani mutumi sanye da kakin rundunar da aka yi bidiyonsa yana shan shisha

- A cewar rundunar, dabi'un da mutumin ya nuna a cikin bidiyon, ya saba da koyarwa, al'adu da dabi'un rundunar 'yan sanda

- Rundunar ta kuma mika bidiyon ga kwararru don gano ko da gaske jami'inta ne, ko sojan gona, ko kuma dai bidiyon sashe ne na wasan kwaikwayo

Rundunar 'yan sanda ta fara bincike kan wani bidiyo da ya karade yanar gizo da ke nuna wani mutumi sanye da kakin rundunar yana shan shisha.

Rundunar a shafinta na Twitter, a ranar Lahadi ta bayyana cewa ta mika bidiyon ga sashen kwararru don gano gaskiyar bidiyon, da kuma sanin mutumin.

A cewar rundunar, gano gaskiyar bidiyon da sanin mutumin, zai tabbatar da cewa ko da gaske jami'in rundunar ne, ko sojan gona, ko kuma dai wani sashe ne na wasan kwaikwayo.

KARANTA WANNAN: Sabon kwamishinan rundunar 'yan sandan FSARS na kasa ya kama aiki

Bidiyo: Rundunar yan sanda ta fara farautar jami'inta da aka nuna yana shan shisha

Bidiyo: Rundunar yan sanda ta fara farautar jami'inta da aka nuna yana shan shisha
Source: Twitter

Sai dai, rundunar ta ce a lokacin da take ci gaba da bincike, ya zama wajibi al'umma su sani cewa dabi'un mutumin da ke cikin bidiyon ba koyarwar rundunar 'yan sanda ba ce.

"Kasancewarmu rundunar tsaro da kuma tabbatar da bin doka da oda, wannan dabi'ar ya saba da koyarwarmu, al'adunmu da kuma horonmu," a cewar rundunar.

A dalilin hakan, rundunar 'yan sanda ta roki 'yan Nigeria da su tuntubi rundunar da zaran sun samu muhimman bayanai da zasu taimaka wajen gano mutumin.

KARANTA WANNAN: Amfanin da lemon tsami ya ke da shi ga lafiyar maniyi

Sabon kwamishinan 'yan sanda da zai ja ragamar sashen rundunar na musamman don dakile fashi da makami (FSARS), CP Imohimi Edgal, ya kama aiki.

CP Imohimi, sabon shugaban rundunar ta FSARS, ya wallafa lambobin da 'yan Nigeria za su rika kira da zaran sun ga ana ayyukan ta'addanci a fadin kasar.

Lambobin kira don mika korafin sune kamar haka: 08121226468, 08081911644 da kuma 09095097307, 08055911306 da kuma 08062856290.

Rahotanni sun bayyana cewa Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda ya nada Edgal shugaban rundunar FSARS domin dakile ayyukan ta'addanci a fadin kasar.

Nasarorin Edgal na dakile ta'addanci a lokacin da ya ke kwamishinan 'yan sanda na jihar Lagos ya sa ya yi kaurin suna daga Satumbar 2017 zuwa watan Maris 2019.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel