Ndume ya jinjiinawa rundunar sojoji a kan samar da tsaro da tallafi

Ndume ya jinjiinawa rundunar sojoji a kan samar da tsaro da tallafi

- Sanata Mohammed Ali Ndume na jam'iyyar APC daga jihar Borno, ya bayyana ire-iren kokarin dakarun sojin Najeriya a yankin

- Shugaban kwamitin kula da rundunar sojin a majalisar dattawa, ya ce baya ga samar da tsaro, akwai ayyukan taimako da jin kai da sojin ke yi wa yankin

- Ya sanar da yadda aka yi jarabawar WAEC a karo na farko cikin shekaru shida, duk a cikin kokarin zakakuran sojojin

Shugaban kwamitin kula da rundunar sojin Najeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume, na jam'iyyar APC da ke wakiltar jihar Borno ta Kudu, ya jinjinawa kokarin rundunar sojin Najeriya.

Ya sanar da cewa, suna iyakar kokarinsu wurin yaki da rashin tsaro a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabas na kasar nan, inda mayakan ta'addanci suka yi katutu.

Ndume wanda ya tabbatar da cewa rundunar sojin bayan yaki da rashin tsaro suna kokarin tabbatar da ganin dawowar 'yan gudun hijira zuwa gidajensu a Borno.

Ya sanar da yadda sojojin suke kokarin samar da kayan rage radadi ga mazauna yankin domin ganin sun koma rayuwarsu kamar yadda suke a da kafin kafuwar ta'addanci.

Tsohon shugaban majalisar ya sanar da cewa, bai dade da dawowa daga zagayen mazabarsa, ya ce rundunar sojin ta cancanci jinjina a kan yadda tsaro yake tabbata na rayuka da kadarori.

KARANTA: Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade a bangaren wutar lantarki

Ndume ya jinjiinawa rundunar sojoji a kan samar da tsaro da tallafi

Ndume ya jinjiinawa rundunar sojoji a kan samar da tsaro da tallafi. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Sabon harin 'yan bindiga: Mutum 2 sun rasu, an kone gidaje masu yawa a Kaduna

Ya ce kokarin sojin ne ya kai ga an rubuta jarabawar kammala sakandare a karo na farko cikin shekaru shida a yankin.

A yayin zantawa da manema labarai a Abuja, Ndume wanda yace baya ga samar da tsaro, sojojin suna koyar da yara 'yan makaranta a Chibok da wasu wurare a Borno.

Ya ce rundunar sojin sun yi wa jama'a burtsatse, gyaran gine-gine da aka kone tare da bai wa jama'a matafiya kariya.

A wani labari na daban, kungiyar dattawan arewa a ranar Lahadi da dare ta bayyana dalilinta na tattaunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo tare da kungiyar Afenifere.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce sun tattauna da su domin shawo kan matsaloli da manyan kalubale da ke addabar kasar nan, Daily Trust ta wallafa.

An yi taron da Obasanjo, shugabannin kungiyar Afenifere, dattawan arewa, ohaneze Ndigbo da wata kungiyar 'yan yankin Neja Delta, sun yi taron tattaunawa na tsawon kwanaki biyu a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel