Kishi: Matashi ya kashe tsohuwar budurwarsa bayan ya dade sanar da jama'a zai kasheta

Kishi: Matashi ya kashe tsohuwar budurwarsa bayan ya dade sanar da jama'a zai kasheta

- Wani matashi mai shekaru 30 a duniya mai suna David ya sossoka wa tsohuwar budurwarsa wuka sakamakon bakin kishi

- Matashiyar mai shekaru 23 ta sheka lahira bayan da tayi sabon saurayi kuma tsohon saurayin ya dinga bibiyarta

- Ya dauketa inda ya kaita har kabarin mahaifiyarsa tare da yi mata alkawarin kasheta da kansa

Wani matashi mai shekaru 30 ya shiga hannun jami'an tsaro a hammanskraal, yankin arewacin Pretoria sakamakon zarginsa da ake da soka wa tsohuwar budurwarsa wuka har ta mutu.

Matashin ya kashe tsohuwar budurwarsa har lahira bayan ta yi sabon saurayi, kamar yadda jami'an 'yan sandan yankin Guateng suka sanar a ranar Lahadi 13 ga watan Satumban 2020.

Matashiyar mai shekaru 23 ta matukar shan wahala sakamakon sossoka mata wuka da tsohon saurayinta yayi bayan kwashe dongon lokacin da yayi yana sanar da jama'a cewa sai ya kasheta.

Kakakin rundunar 'yan sandan yankin, Kyaftin Kay Makhubele wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Ya ce mutumin mai suna David Setshoa ya soki budurwa mai shekaru 23 mai suna Thato da wuka a wani lamari da ake zargin kishi ne.

Lamarin ya faru a Leboneng a ranar Alhamis da yammaci. An kama shi a ranar Juma'a kuma ana tsammanin za a gurfanar da shi a gaban wata kotun majistare da ke Temba a ranar Litinin 14 ga watan Satumba.

An gano cewa, David ya dinga bibiyar lamarin Thato tun bayan rabuwarsu, kuma ta samu sabon saurayi.

KU KARANTA: Magidancin da ke lalata da 'ya'yansa 4 mata ya ce ubangiji ya halasta mishi hakan

Kishi: Matashi ya kashe tsohuwar budurwarsa bayan ya dade sanar da jama'a zai kasheta

Kishi: Matashi ya kashe tsohuwar budurwarsa bayan ya dade sanar da jama'a zai kasheta. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Jerin sunaye: Buhari ya yi sabbin nade-nade a bangaren wutar lantarki

Kamar yadda majiyoyi makusanta suka sanar, yana yawan sanar da cewa sai ya kasheta.

"David Setshoa tsohon saurayin Thato Gadebe ya sossoka mata wuka a Themba, Hamanskraal. Tun farko budurwarsa ce amma sun rabu sai ta hadu da wani," jaridar Daily Talk ta ruwaito.

"Tsohon saurayin nata yana bibiyarta tun bayan da ta hadu da wani saurayi. An gano cewa ya tsareta a yayin da taje wani babban kanti tare da sabon saurayinta.

"An kira 'yan sanda amma sai suka ce ai babu abinda yayi mata amma za su bata kariya daga wanda ake zargin.

"Muna da tabbacin cewa David ya dinga yunkurin kasheta tun a baya. An zargesa da kai Thato har kabarin mahaifiyarsa kuma ya yi alkawarin kasheta da kansa.

"Akwai wani lokaci na daban da yayi kokarin tsallaka katanga ya shiga wurinta yayin da yake dauke da bindiga," rahoton yace.

A halin yanzu, kawaye, 'yan uwa da abokan arziki sunata ta jajen tare da makokin mutuwarta tare da bukatar daukar mataki a kan wanda ake zargin.

A wani labari na daban, a ranar Alhamis ne 10 ga watan Satumba, wani Malamin Islamiyya dake zaune a Ibadan mai suna, Naheem Salami, ya bayyanawa wata kotu dake a Ibadan, jihar Oyo, cewa matarshi mai suna Taiwo, tana sulalewa daga kan gadonsu a lokacin da suke kwance da daddare, tana zuwa dakin makwabcinsu wanda yake gwauro ne ba shi da aure.

Salami, wanda ya isa kotu a bisa karar shi da Taiwo ta kai gaban kotu akan a raba aurensu, ya bayyana cewa matarshi muguwar mata ce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel