Gayyatar DSS: Rayuwata tana cikin babban hatsari - Mailafia ya koka

Gayyatar DSS: Rayuwata tana cikin babban hatsari - Mailafia ya koka

- Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailafia, ya tabbatar da cewa rayuwarsa na cikin hatsari da garari

- Ya sanar da cewa hukumar jami'an tsaro na farin kaya sun sake gayyatarsa a karo na uku kuma zai je a ranar Litinin da karfe 11 na safe

- Ya ce yana da tabbacin maganar da yayi a kan kisan kananan yara, mata da matasa ne yasa wasu 'yan siyasa suke fatan rufe masa baki har abada

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailafia, ya ce rayuwarsa tana cikin garari tare da hatsari.

Mailafia ya sanar da hakan ne a yayin da yake martani a kan gayyatar da jami'an tsaro na farin kaya suka yi masa a karo na uku.

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin, a wata takarda da ya fitar a Jos a ranar Juma'a, ya kwatanta gayyatar DSS da siyasa. Ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su yi masa addu'ar kariya.

Ya ce, "An kira ni a karo na uku da in bayyana a gaban jami'an tsaro na farin kaya da ke Jos wannan Litinin mai zuwa, 14 ga watan Satumba da karfe 11 na safe.

"Baya da irin gwagwarmayar da muke yi a kotu, lauyana ya bayyana a gaban babbar kotu da ke Jos a ranar Juma'a.

"Na kwashe sama da shekaru 20 ina aiki a kasar ketare a matsayin malami, ma'aikacin banki da kuma ma'aikacin gwamnati ba tare da wani mugun tarihi ba.

"Bani da wani mummunan tarihi ko kadan. Amma abun takaici shine yadda a kasata ake bincikata da mugun laifi mai cike da siyasa a ciki."

KU KARANTA: Sai muna kwance ni da ita sai ta sulale zuwa dakin wani gardi suyi iskanci - Malamin Islamiyya ya kai matar shi kara kotu

Gayyatar DSS: Rayuwata tana cikin babban hatsari - Mailafia ya koka
Gayyatar DSS: Rayuwata tana cikin babban hatsari - Mailafia ya koka. Hoto daga Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kana taka Allah na tashi: Ango ya mutu kwanaki kadan bayan ya auri kyakkyawar amaryar shi

"Ina barar addu'arku. Ina da dalilan da suka sa nace rayuwata tana cikin hatsari, kuma wasu 'yan siyasa ne suke son kashe min baki na har abada saboda fadin gaskiya.

"Saboda magana da nayi a kan wadanda suka yi shahada. Dubban kananan yara, mata, dattawa da matasa da aka kashe a kasata.

“Ina kira ga jama'ar da ke Jos ko wadanda za su iya zuwa Jos da su zo da yawansu domin bani goyon baya a ranar Litinin da karfe 11 na safe. Amma kada wanda ya wurga koda dutse ne a madadina. Ina muku fatan alkhairi," yace.

A wani labari na daban, Legit.ng ta bayyana cewa, Dr Mailafia ya sanar da cewa wani gwamnan arewa ne yake daukar nauyin Boko Haram.

Lamarin da yasa hukumar jami'an tsaro ta farin kaya suka gayyacesa domin neman karin bayani

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel