Magidancin da ke lalata da 'ya'yansa 4 mata ya ce ubangiji ya halasta mishi hakan

Magidancin da ke lalata da 'ya'yansa 4 mata ya ce ubangiji ya halasta mishi hakan

- Wata kotun majistare ta gurfanar da wani dattijo mai shekaru 64 a duniya sakamakon lalata da yake yi da 'ya'yansa mata hudu

- Ana zargin Archibong da laifin lalata da 'ya'yansa mata hudu inda yake tsoratar da su da yunwa idan basu amince ba

- Ya sanar da su cewa a littafin bibul, Luth yana saduwa da 'ya'yansa mata hudu kuma ubangiji bai yi fushi da shi ba

Wani dattijo mai shekaru 64 mai suna Bassey Archibong da ke gida mai lamba 10 a titin Dipo, yankin Owutu da ke Ikorodu a jihar Legas ya gurfana a gaban kotu.

Ana zargin Archibong da laifin yi wa 'ya'yansa mata har hudu fyade masu shekaru 12 zuwa 20 a duniya, Vanguard ta wallafa.

An gano cewa Archibong ya saba ma'amala muguwa da 'ya'yansa mata tun a 2016. An gurfanar da shi a kan laifuka uku da suka hada da lalata da 'ya'yansa a gaban wata kotun majistare da ke Legas.

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su.

Dan sanda mai gabatar da kara, John Iberedem, ya ce Archibong yana amfani da abinci wurin jan ra'ayin yaran domin ya yi lalata da su.

Iberedem ya ce, a duk lokacin da yaran suka ki amincewa da shi, ya kan janyo musu ayoyi daga bibul inda Luth yake mu'amala da 'ya'yansa mata kuma Ubangiji bai ladabtar da shi ba.

Iberedem ya ce wannan laifin ya ci karo da sashi na 265 sakin layi biyu na dokokin jihar Legas na 2019.

KU KARANTA: Hotuna: Magoya bayan APC sun ragargza shagunan wasu 'yan kasuwa da suka koma PDP

Magidancin da ke lalata da 'ya'yansa 4 mata ya ce ubangiji ya halasta mishi hakan

Magidancin da ke lalata da 'ya'yansa 4 mata ya ce ubangiji ya halasta mishi hakan. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Sai muna kwance ni da ita sai ta sulale zuwa dakin wani gardi suyi iskanci - Malamin Islamiyya ya kai matar shi kara kotu

Ya ce, "Wanda ke kare kansa yana dukan 'ya'yansa sannan ya hana su abinci a duk lokacin da suka tambayeshi dalilin da yasa yake lalata da su.

"Yana sanar da su cewa lalata tsakanin 'ya'ya da mahaifinsu ba komai bane, ubangiji ya amince da hakan.

"Ya sanar da yaran cewa ubangiji zai kona su matukar suka ki amincewa da shi, kuma ba zai taba ladabtar da shi ba domin ya kusancesu."

Alkalin kotun, F. A Azeez, ya bada umarnin cigaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari har zuwa ranar 30 ga watan Oktoba da za a ci gaba da sauraron karar.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama masu fyade har mutum 140 a jihar.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Sanusi Buba, shine ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis lokacin da yayi hira da su.

Ya ce an kama masu laifin a kararraki 87 da aka kai cikin kananan hukumomi 34 na fadin jihar. Kwamishinan ya ce an dauki wadannan rahotanni nasu ne a cikin tsakiyar wannan shekarar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel