Yanzu-yanzu: Sabon kwamishinan rundunar 'yan sandan FSARS na kasa ya kama aiki

Yanzu-yanzu: Sabon kwamishinan rundunar 'yan sandan FSARS na kasa ya kama aiki

- An nada CP Imohimi Edgal, a matsayin sabon shugaban sashen rundunar 'yan sanda na musamman, da ke dakile fashi da makami (FSARS)

- Sabon kwamishinan rundunar ta FSARS, ya bayar da lambobin da 'yan Nigeria za su rika kira da zaran sun ga ana aikata ayyukan ta'addanci

- Lambobin kira don mika korafin sune kamar haka: 08121226468, 08081911644 da kuma 09095097307, 08055911306 da kuma 08062856290

Sabon kwamishinan 'yan sanda da zai ja ragamar sashen rundunar na musamman don dakile fashi da makami (FSARS), CP Imohimi Edgal, ya kama aiki.

CP Imohimi, sabon shugaban rundunar ta FSARS, ya wallafa lambobin da 'yan Nigeria za su rika kira da zaran sun ga ana ayyukan ta'addanci a fadin kasar.

Lambobin kira don mika korafin sune kamar haka: 08121226468, 08081911644 da kuma 09095097307, 08055911306 da kuma 08062856290.

KARANTA WANNAN: Shugaban kasa Buhari: Noma shi ne mafita ga matasa masu jini a jika

Yanzu-yanzu: Sabon kwamishinan rundunar 'yan sandan FSARS na kasa ya kama aiki

Yanzu-yanzu: Sabon kwamishinan rundunar 'yan sandan FSARS na kasa ya kama aiki
Source: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda ya nada Edgal shugaban rundunar FSARS domin dakile ayyukan ta'addanci a fadin kasar.

Nasarorin Edgal na dakile ta'addanci a lokacin da ya ke kwamishinan 'yan sanda na jihar Lagos ya sa ya yi kaurin suna daga Satumbar 2017 zuwa watan Maris 2019.

A lokacin da ya ke kwamishinan yan sandan Lagos, 'yan fashi da makami da masu aikata miyagun laifuka sun samu matsin lamba, al'umar jihar ba zasu taba mantawa da shi ba.

KARANTA WANNAN: Tashin farashin man fetur da lantarki: Shawarar da Kwankwaso ya ba Buhari

Daga cikin bangarorin ta'addanci da ya fi mayar da hankali akwai fashi da makami, garkuwa da mutane, kungiyoyin asiri, cin zarafin kananan yara da mata da masu safarar miyagun kwayoyi.

Har yanzu ana tuna Edgal a jihar Lagos saboda tarihin da ya kafa na kakkabe yan ta'adda a tsawon watanni 18 da ya yi a matsayin kwamishinan 'yan sandan jihar.

Kasancewar ya rike mukamin kwamishinan yan sanda da kuma mukamin mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da ayyukan ta'addanci, Edgal, ya saba da wannan aiki.

A wani labarin, Rundunar soji ta yi bajakolin dumbin miyagun makamai da ta samu bayan sun kashe shararren dan ta'adda, Terwaze Akwaza wanda aka fi sani da 'Gana', a jihar Benuwe.

Kafin a kashe shi ranar Talata, an taba saka ladan miliyan N10 a kan duk wanda zai bayar da wata gudunmawa da zata kai ga kama Gana, wanda ya addabi jihohin Benuwe, Nasarawa da Taraba da aikata miyagun laifuka.

Rundunar sojin Nigeria da ke atisayen AYEM APKATUMA III ta bayyana yadda ta kashe gagararren dan ta'addan Benue, Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Gana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel