Tashin farashin man fetur da lantarki: Shawarar da Kwankwaso ya ba Buhari

Tashin farashin man fetur da lantarki: Shawarar da Kwankwaso ya ba Buhari

- Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya janye karin farashin lantarki da man fetur

- Kwankwaso ya ce karin farashin fetur da lantarki, zai kara jefa talakawan kasar cikin mawuyacin hali

- Haka zalika, Kwankwaso ya shawarci Buhari da ya daina tatsar 'yan Nigeria, da sunan tara kudadewa kasar, ta hanyar kakaba haraji

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa karin farashin man fetur da wutar lantarki a wannan lokacin zai kara jefa 'yan Nigeria cikin mawuyacin hali.

Ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta janye karin, yana mai cewa kamata ya yi shugaban ya dinke barakar da ake samu a gwamnatinsa maimakon karin farashin man fetur da lantarki.

Kwankwaso wanda ya yi wannan kiran a zantawarsa da BBC Hausa ranar Juma'a ya ce babu wani kwakkwaran dalili na kara kudin fetur da lantarki.

KARANTA WANNAN: Janye tallafin man fetur: Gwamnatin tarayya ta fadi ayyukan da zata yi da kudaden

Tashin farashin man fetur da lantarki: Shawarar da Kwankwaso ya ba Buhari

Tashin farashin man fetur da lantarki: Shawarar da Kwankwaso ya ba Buhari
Source: Twitter

Ya ce, "Mafi akasarin kasashen duniya suna samar da hanyoyin tallafawa al'umarsu don rage radadin COVID-19, amma a Nigeria, sai ma kara farashin lantarki da fetur aka yi.

"Zai yi matukar wahala ka samu wanda ke goyon bayan wannan tsarin da gwamnatin tarayyar ta aiwatar," a cewar sa.

Tsohon gwamnan wanda kuma jigo ne a jam'iyyar adawa ta PDP, ya yi gargadin cewa karin kudaden zai janyo yunwa, rashin tsaro da kuma rashin ayyukan yi a kasar.

Tsohon ministan tsaron kuma tsohon sanata ya ce babu wata illa da zata iya biyo baya idan har gwamnati ta janye karin farashin, kuma hakan al'ummar kasar ke bukata.

KARANTA WANNAN: Farashin burodi zai yi tashin gwauron Zabi - masu gidajen burodi sun sanar

Kwankwaso ya bukaci shugaban kasar da ya daina abunda ya kira da tatsar 'yan Nigeria ta hanyar kakaba masu haraji mai yawa.

"Gudanar da harkokin gwamna na bukatar kudaden shiga da ayyukan yi, don haka abun da ya fi dacewa gwamnati ta yi shi ne daina tatsar al'umar kasar da sunan haraji," a cewar sa.

Tsohon gwamnan wanda a yanzu ya ke jihar Edo domin karfafa yakin zaben jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar da za a gudanar karshen makon nan.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa gwamnatin tarayya ta kara farashin wutar lantarki da man fetur.

Gwamnatin ta ce karin kudaden ya zama tilas saboda karyewar tattalin arzikin kasa da ya faru sakamakon barkewar annobar COVID-19.

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta ce janye tallafin man fetur zai taimaka mata wajen samun sama da N1trn a kowanne wata, don bunkasa kasar.

Ministan cikin gida kan ma'adanan man fetur, Timipre Sylva, ya shaidawa manema Labarai hakan a ranar Alhamis.

Timipre Sylva ya tabbatar da cewa, da kudaden da gwamnati za ta samu na janye tallafin man fetur din, za ta gyara matatun man fetur na kasar, wanda zai kai ga samar da ayyukan yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel