Janye tallafin man fetur: Gwamnatin tarayya ta fadi ayyukan da zata yi da kudaden

Janye tallafin man fetur: Gwamnatin tarayya ta fadi ayyukan da zata yi da kudaden

- Gwamnatin Nigeria ta bayyana dalilin da ya sanya ta janye tallafin man fetur, da kuma ayyukan da za ta yi da rarar kudaden

- Ministan man fetur, Timipre Sylva ya bayyana cewa za a gyara matatun man fetur na kasar, wanda zai samar da ayyukan yi ga matasan kasar

- Ministan ya ce lokaci ya yi da ya kamata 'yan Nigeria su fahimci gaskiya, kuma su yi abunda ya dace

Gwamnatin tarayya ta ce janye tallafin man fetur da yin garambawul a masana'antar zai taimaka mata wajen samun sama da N1trn a kowanne wata, don bunkasa kasar.

Ministan cikin gida kan ma'adanan man fetur, Timipre Sylva, ya shaidawa manema Labarai hakan a ranar Alhamis.

Timipre Sylva ya tabbatar da cewa, da kudaden da gwamnati za ta samu na janye tallafin man fetur din, za ta gyara matatun man fetur na kasar, wanda zai kai ga samar da ayyukan yi.

KARANTA WANNAN: Farashin burodi zai yi tashin gwauron Zabi - masu gidajen burodi sun sanar

Janye tallafin man fetur: Gwamnatin tarayya ta fadi ayyukan da zata yi da kudaden
Janye tallafin man fetur: Gwamnatin tarayya ta fadi ayyukan da zata yi da kudaden
Asali: Twitter

"Dangane da maganar matatun mai; kudurinmu shi ne farfado da matatun man fetur. Za mu fara da matatar man fetur ta garin Fatakwal.

"A Fatakwal, muna da matatun mai guda biyu; tsohuwar matatar da kuma sabuwa, wadanda za su iya tace ganga 60,000 da 250,000 a kowacce rana.

"A yanzu, za a samar da matatar mai ta uku a Fatakwal wacce za ta zama sha kundum, amma za ta kasance ta 'yan kasuwa a cikin Fatakwal din.

KARANTA WANNAN: Miji ya yanke shawarar sakin matarsa bayan gano kwaroron roba 23 a bandaki

"Za a sa hannu kan wannan aikin a zango na hudu na shekarar 2020. Kuma a zangon karshe na 2021, mu ke sa ran matatar za ta fara aiki. Muna tattauna farfado da matatar Warri da Kaduna.

"Lokaci ya yi da ya kamata 'yan Nigeria su fahimci gaskiya, kuma su yi abunda ya dace. Shin me nene amfanin janye tallafin man fetur din? Za mu samu rarar kudade masu yawa.

"Akalla, zai sa mu samu rarar akalla tiriliyan daya a kowacce shekara. Tuni dai, mun yi bayanin hakan a cikin kasafin kudin da ya shafi janye tallafin, da ya kai N500bn a kasafin," a cewar ministan.

A wani labarin, kungiyar masu gidajen burodi guda biyu, PBAN da kuma AMBCN, sun koka kan yadda farashin kayan da suke sarrafa burodin ya tashi a kasuwa.

Kungiyoyin, a taron manema labarai a Lagos, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba tashin farashin kayan masarufin, don daukar matakin ragewa.

A cewar su, tashin farashin kayan sarrafa burodin "na dab da shafe masana'antar samar da burodi a Nigeria."

Shugaban kungiyar PBAN, Tosan Jemide, a zantawarsa da manema labarai a ranar Alhamis, ya ce masana'antar samar da burodin ta samawa miliyoyin 'yan Nigeria aikin yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel