Wata sabuwa: Farashin burodi zai yi tashin gwauron Zabi - masu gidajen burodi sun sanar

Wata sabuwa: Farashin burodi zai yi tashin gwauron Zabi - masu gidajen burodi sun sanar

- Kungiyar masu gidajen burodi sun koka kan yadda farashin kayan da suke sarrafa burodin ya tashi a kasuwa

- Mambobin kungiyar sun ce ba za su iya jure wannan karin farashin kayan abincin ba, dole su ma su kara farashin burodin

- Mr Jemide ya koka kan yadda masana'antun sukari, fulawa da kayayyakin sarrafa burodin suka kara farashin kayansu

Kungiyar masu gidajen burodi guda biyu, PBAN da kuma AMBCN, sun koka kan yadda farashin kayan da suke sarrafa burodin ya tashi a kasuwa.

Kungiyoyin, a taron manema labarai a Lagos, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba tashin farashin kayan masarufin, don daukar matakin ragewa.

A cewar su, tashin farashin kayan sarrafa burodin "na dab da shafe masana'antar samar da burodi a Nigeria."

Shugaban kungiyar PBAN, Tosan Jemide, a zantawarsa da manema labarai a ranar Alhamis, ya ce masana'antar samar da burodin ta samawa miliyoyin 'yan Nigeria aikin yi.

KARANTA WANNAN: Miji ya yanke shawarar sakin matarsa bayan gano kwaroron roba 23 a bandaki

Wata sabuwa: Farashin burodi zai yi tashin gwauron Zabi - masu gidajen burodi sun sanar
Wata sabuwa: Farashin burodi zai yi tashin gwauron Zabi - masu gidajen burodi sun sanar
Asali: UGC

Tosan Jemide ya yi jawabi ne a madadin kungiyoyin guda biyu.

"Kuma tana daga cikin manyan masana'antun da suke samar da ayyukan yi kai tsaye a kasar."

Mr Jemide ya yi nuni da cewa burodi a yanzu ya zama ruwan dare a abincin da 'yan Nigeria ke ci, ba tare da banbancin arziki ko talauci ba, kuma yana taka rawa a bangaren tattalin arziki.

"Duk da cewa muna samun matsaloli da dadewa, farashin fulawa daga watan Maris 2020 da Agusta 2020 ya tashi daga N10,500 zuwa N13,500 a kowanne buhu mai 50kg.

"Farashin sukari ya tashi daga N13,500 zuwa N29,000, daga bisani ya dawo N19,000 a kan kowanne buhu daya.

"Sinadarin Margarine ana sayar da shi N5,800 amma yanzu ya dawo N11,000. Lita 25 na man gyada ya tashi daga N13,000 zuwa N16,000 yayin da madarar N29,000 ta koma N52,000 a buhu.

"Sinadarin Calcium ya tashi daga N25,000 zuwa N34,500, kuma da tunanin cewa farashin kayayyakin zai iya tashi nan gaba," a cewar sa.

Mr Jemide ya kara da cewa mambobin kungiyar sun dade suna sarrafa burodin tare da sayar da shi ba tare da kara masa kudi ba duk da karuwar farashin kayan masarufin.

KARANTA WANNAN: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar wadatar da kasa da abinci

Sai dai ya ce a halin da ake ciki yanzu, mambobin kungiyar sun ce ba za su iya jure wannan karin farashin kayan abincin ba, dole su ma su kara farashin burodin.

Ya ce, "Da yawanmu muna karbo basussuka daga bankuna domin tafiyar da sana'ar burodin, amma gaskiya mukan gaza biyan basussukanmu, saboda tsadar kayan masarufin.

"Gaskiya daga yau ba zamu iya jure karin farashin sukari, fulawa, da sauran kayan da muke sarrafa burodin ba, muma ya zama wajibi mu kara farashin burodin."

Mr Jemide ya koka kan yadda masana'antun sukari, fulawa da kayayyakin sarrafa burodin suka kara farashin kayansu, ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki a masana'antar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel