Da duminsa: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar wadatar da kasa da abinci

Da duminsa: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar wadatar da kasa da abinci

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya jagoranci zaman majalisar wadatar da kasa da abinci NFSC

- A jawabin shugaban kasar, ya ce wadatar da kasar da abinci na daga cikin kudurorin gwamnatinsa, kuma zai tabbatar an cimma hakan

- Rahotanni sun bayyana cewa a yayin taron, majalisar ta tattauna kan tashin farashin kayan abinci a kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya jagoranci zaman majalisar wadatar da kasa da abinci NFSC tare da gwamnoni 6.

Daga cikin mahalarta taron akwai shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da wasu ministocin kasar.

Taron ya hada da mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) da kuma Darakta Janar na sashen tsaron DSS, Yusu Bichi.

KARANTA WANNAN: Hukumar kwastam ta samu fiye da biliyan ₦9 a cikin wata 8

Da duminsa: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar wadatar da kasa da abinci
Da duminsa: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar wadatar da kasa da abinci
Asali: Twitter

A jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taron, ya ce wadatar da kasar da abinci na daga cikin kudurorin gwamnatinsa.

Dangane da ambaliyar ruwan sama da ta shafi wasu jihohin Nigeria, shugaban kasar ya jajantawa wadanda lamarin ya shafa, ya ce gwamnatinsa za ta duba illar da hakan ya yi.

"Ina son na sanar da 'yan Nigeria cewa gwamnati na a shirye take ta taimakawa manoman da suke da fasaha da kimiyyar yin noma, don samar da wadataccen abinci a kasar."

Dangane da karancin gonaki da ake samu sakamakon yawaitar masu shigar harkar noma da kuma bunkasa shi, shugaban kasar ya ce za a duba yiyuwar fadada filaye da gonaki.

Haka zalika shugaba Buhari ya sha alwashin bunkasa fannin tsaro, don kare harkar noma, a kan hakan ne ma gwamnatinsa ta dauki hayar sojojin gona a sassa daban daban na kasar.

"La'akari da karyewar tattalin arziki, mun dauki matakan bayar da basussuka ga manoma da kuma gina tituna. Mun kuma yi shiri na alkinta abincin da manoman mu ke shukawa."

KARANTA WANNAN: Rashin tsaro: Fiye da Katsinawa 2,226 sun yi hijira zuwa Gombe

Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa a yayin taron, majalisar wadatar da kasar da abinci ta tattauna kan tashin farashin kayan abinci a kasar.

A wani labarin, Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da 'Kwastam' ta samu rabanu na biliyan ₦976.6 daga watan Janairu zuwa Agusta na shekarar 2020.

A wata takarda da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa ranar Alhamis, an nuna cewa an samu kudaden ne daga rabanu a kan kayan da aka shigo dasu Najeriya da kudin duti da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel