Zuwan COVID-19 wa'azine a garemu, ya kamata mu koma ga Allah - Gwamna Sanwo-Olu

Zuwan COVID-19 wa'azine a garemu, ya kamata mu koma ga Allah - Gwamna Sanwo-Olu

-Gwamna Sanwo-Olu, ya ce annobar Covid-19 ta koyawa 'yan Nigerida darasi mai yawa, sannan akwai bukatar a koma ga Allah

- Sanwo-Olu, wanda ya ce adadin masu kamuwa da cutar kullum na raguwa a jihar, ya kuma jajantawa wadanda suka rasa 'yan uwansu

- Babban malamin coci na Lagos, Rt. Rev. Humphrey Olumakaiye, a jawabinsa, ya godewa wadanda suka halarci wannan taron

Gwamnan jihar Lagos, Mr Babajide Sanwo-Olu, a ranar Litinin ya ce annobar Covid-19 ta koyawa 'yan Nigerida darasi mai yawa, sannan akwai bukatar a koma ga Allah.

Sanwo-Olu, wanda ya bayyana hakan a taron bude bukin rantsar da malaman coci karo na 34 a Lagos, ya kuma bukaci al'umma da su ci gaba da addu'a ga jihar da kasa baki daya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa sashe na biyu na taron rantsarwar malaman cocin karo na 34 ya gudana ne a cocin Our Saviours, filin wasannin Tafawa Balewa, jihar Lagos.

KARANTA WANNAN: Bayan shekaru 22; Kifin da daliban jami'a ke neman sa'ar jarrabawa a wurinsa ya mutu

Zuwan COVID-19 wa'azine a garemu, ya kamata mu koma ga Allah - Gwamna Sanwo-Olu
Zuwan COVID-19 wa'azine a garemu, ya kamata mu koma ga Allah - Gwamna Sanwo-Olu
Source: Twitter

"COVID-19 ta nuna mana gaskiya kan bukatar mu dage da addu'a. Har yanzu bamu fita daga cikinta ba, akwai bukatar ci gaba da daukar matakai. Addu'o'i ne kawai ke tasiri a yanzu.

"Cocin ta shiga cikin shirye shirye da dama a lokacin da ake kulle, ta bayar da tallafi ga mabukata daga cikin al'umar jihar, ina godewa kowacce coci da hakan," a cewar sa.

KARANTA WANNAN: An kama 'yan Najeriya hudu da laifin damfarar Banki a kasar waje

Sanwo-Olu, wanda ya ce adadin masu kamuwa da cutar kullum na raguwa a jihar, ya kuma jajantawa wadanda suka rasa 'yan uwansu sakamakon cutar.

Ya ce an zabi taken taron, "Addu'a, Ibada da Dorewa', la'akari da yadda annobar ke ci gaba da yin barna a fadin duniya."

Haka zalika, ya jinjinawa ma'aikatan kiwon lafiya bisa namijin kokarinsu na aiki ba dare ba rana domin ganin an shawo kan wannan annoba.

Babban malamin coci na Lagos, Rt. Rev. Humphrey Olumakaiye, a jawabinsa, ya godewa wadanda suka halarci wannan taron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel