Talauci da lalacewar tattalin arziki na karuwa a kowacce rana a Najeriya - Osinbajo

Talauci da lalacewar tattalin arziki na karuwa a kowacce rana a Najeriya - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jajanta halin talaucin da kasar nan ke ciki tare da karairayewar tattalin arziki hadi da matsin rayuwa da annobar korona ta ke janyowa a kullum.

Kamar yadda ya sanar a wata takardar da ya fitar a ranar Talata hannun kakakinsa, Laolu Akande, mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin taron duba yanayin aikin ministoci na shekara da da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Kamar yadda taken takardar ya bayyana, "Mataimakin shugaban kasa ga ministoci: Bukatar gaggauta amfani da kudin rage radadin da gwamnati na ware."

A takardar, mataimakin shugaban kasa ya ce, "A halin yanzu muna rana ta 67 tun bayan fara shirin. Babu abinda zai faru kamar sihiri, dole ne mu yi komai da kanmu."

"Dole mu tabbatar da cewa muna da kudin kuma muna duba ci gaban da ake samu a kowacce rana. Ta hakan ne za'ayi abinda ya dace a lokaci da ya dace.

"Hakazalika, lokaci ba zai sassauta mana ba. A kowacce rana talauci karuwa yake kuma tattalin arziki na sake yin kasa."

Talauci da lalacewar tattalin arziki na karuwa a kowacce rana a Najeriya - Osinbajo
Talauci da lalacewar tattalin arziki na karuwa a kowacce rana a Najeriya - Osinbajo. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Yaro mai shekaru 11 yayi ceton rai, ya tuka kakarsa a mota zuwa asibiti

Osinbajo ya kara da cewa, "Hanya daya ce garemu ta fita daga halin da muke ciki, shine karfafa saar da kayayyakin bukata ta yadda masu bukata za su siya amma da kudaden da muka basu."

Ya ce a karkashin shirin noma da kiwo, gwamnati ta ware naira miliyanahudu domin manoman Najeriya.

A karkashin shirin samar da gidaje, ya yi bayanin cewa gwamnati za ta gina gidaje 300,000 a fadin kasar nan, kuma za ta tabbatar da cewa farashinsu bai zarce naira miliyan biyu ba.

Osinbajo ya ce, an samar da hanyoyin samuwar aiki ga matasa domin rage zaman kashe wando.

KU KARANTA: Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Tarata, ya ce yakamata masu kudin Najeriya su yi wa mulkinsa adalci, Channels TV ta wallafa. Shugaban kasar ya bayyana hakan a yayin rufe taron duba ayyukan ministoci na shekarar farko wanda aka yi a Abuja.

"Ina son in yi kira ga masu hannu da shuni na Najeriya da su yi mana adalci," Buhari yace yayin da yake sanar da cewa mulkinsa ya yi kokari mai yawa duk da rashin kayan aiki.

Ya ce a kalla ana samar da danyen man fetur daga 1999 zuwa 2014, ganga miliyan 2.1 kuma ana siyar da ita a dala dari kowacce ganga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel