Yahoo-yahoo: An kama 'yan Najeriya hudu da laifin damfarar Banki a kasar waje

Yahoo-yahoo: An kama 'yan Najeriya hudu da laifin damfarar Banki a kasar waje

- An cafke wasu dalibai hudu 'yan Nigeria a kasar Philippine bisa zarginsu da laifin yin kutse a na'urar bankunan kasar

- A yayin kutsen, sun yi awon gaba da akalla P100m (N7,900,700.00), inda suka tura kudaden a wani asusun banki daban

- Sai dai, gaba daya 'yan Nigerian hudu, sun musanya wannan zargi da ake yi masu

An cafke wasu dalibai hudu 'yan Nigeria a birnin Muntinlupa, kasar Philippine bisa zarginsu da laifin yin kutse a na'urar bankunan kasar tare da sace kudade.

Sai dai, gaba daya 'yan Nigerian hudu, sun musanya wannan zargi da ake yi masu.

Hukumar binciken kudade ta kasar ta sanar da hakan a ranar Talata, a cewar jaridar ABS CBN News.

Sanarwar na dauke da sa hannun shugaban sashen binciken laifukan kutse ta yanar gizo na hukumar NBI, Vic Lorenzo.

Hukumar binciken ta yi ikirarin cewa an bi diddigin shige da ficen kudaden masu kutsen – 'yan Nigeria – a lokacin da suka yi kutse a na'urar bankin Philippine.

KARANTA WANNAN: Kakar wasanni ta Premier: Matasan 'yan wasa biyar masu tashe a taka leda

Yahoo yahoo: An cafke 'yan Nigeria guda 4 da laifin kutse a na'urar bankin kasar Philippine
Yahoo yahoo: An cafke 'yan Nigeria guda 4 da laifin kutse a na'urar bankin kasar Philippine
Source: Twitter

A yayin kutsen, sun yi awon gaba da akalla P100m (N7,900,700.00), inda suka tura kudaden a wasu asusun bankuna daban daban.

Hukumar ta kuma yi zargin cewa 'yan Nigerian sun karya dokar haramta kutse, dokar ADL, da kuma kutse a takardun bayanan mutane na sirri.

Sai dai NBI a cikin sanarwar sun gaza ambatar sunayen 'yan Nigerian.

Sanarwar ta ce, "Daya daga cikin 'yan matan masu kutsen, ta bayar da shaidar sanya kudi a asusunta, tare da cire akalla P2m, da suka biya kudin makaranta da su.

"An gano katunan ATM da takardun bankuna a hannun wadanda ake zargin."

Yayin da suke musanya wannan zargi, 'yan Nigerian sun shaidawa jaridar ABS CBN cewar suna zama a kasar ne don yin karatu, kuma ba su san da maganar kutse a na'urar bankunan ba.

KARANTA WANNAN: Pakistan ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aika sakon batanci ga Musulmi

"Kudin da muka ciro daga asusun budurwar, wani tallafine daga wata kungiya da take tallafawa dalibai 'yan Nigeria a kasashen waje," a cewar daya daga cikin 'yan Nigerian.

A wani labarin; Wata kotu da ke zama a Gabashin Pakistan, garin Lahore ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aikata laifin batanci, a cewar lauyansa.

Hakan na daga cikin tsauraran matakan da Pakistan ta dauka kan cin zarafi ko batanci ga addinai, musamman marasa karfi.

Asif Pervaiz, (37) ya kasance a kulle tun 2013 a lokacin da aka zarge sa da tura sakonnin batanci ga shugabansa a wajen aiki, lauyansa Saif-Ul-Malook ya shaidawa Al Jazeera.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel