Bayan shekaru 22; Kifin da daliban jami'a ke neman sa'ar jarrabawa a wurinsa ya mutu

Bayan shekaru 22; Kifin da daliban jami'a ke neman sa'ar jarrabawa a wurinsa ya mutu

- Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu, ya shiga sahun ma su ta'aziyyar rasuwar wani kifi da ya mutu a Jami'a ta biyu mafi girma a kasar

- Batun mutuwar kifin, Wanda ake kira da suna 'Mafishi' ta yi fice a manhajar tuwita a dandalin sada zumunta na kasar Zambia

- Wasu daga cikin daliban jami'ar kan ziyarci Kifin kafinsu shiga dakin jarrabawa saboda sun yi imanin ya na bayar da sa'a

Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu, ya shiga sahun ma su ta'aziyyar rasuwar wani kifi da ya mutu a wani tafki da ke Jami'a ta biyu mafi girma a kasar.

Daliban jami'ar Copperbelt (CBU) sun yi zarya a harabar jami'ar yayin da suke dauke da kyandira ma su ci da wuta domin nuna juyayin mutuwar kifin.

Batun mutuwar kifin, Wanda ake kira da suna 'Mafishi' ta yi fice a manhajar tuwita a dandalin sada zumunta na kasar Zambia.

KARANTA WANNAN: An kama 'yan Najeriya hudu da laifin damfarar Banki a kasar waje

Bayan shekaru 22; Kifin da daliban jami'a ke neman sa'ar jarrabawa a wurinsa ya mutu
Bayan shekaru 22; Kifin da daliban jami'a ke neman sa'ar jarrabawa a wurinsa ya mutu
Source: Twitter

Kifin ya rayu tsawon fiye da shekaru 20 kuma dalibai sun yarda yana bayar da sa'ar jarrabawa.

Mafishi na nufin 'babban kifi' a yaren Bemba na kasar Zambia, wacce ke gabashin nahiyar Afrika.

Ana tunanin cewa Mafishi ya rayu na tsawon akalla shekara 22, saboda ya shafe fiye da shekara 20 a koramar da ke Jami'ar, a cewar shugaban kungiyar dalibai, Lawrence Kasonde.

Shugaban kungiyar daliban ya bayyana cewa har yanzu ana binciken dalilin mutuwar kifin.

"Har yanzu ba a binneshi ba, mu na tunanin adanashi a haka," kamar yadda Kasonde ya shaidawa BBC.

Wasu daga cikin daliban jami'ar kan ziyarci Kifin kafinsu shiga dakin jarrabawa saboda sun yi imanin ya na bayar da sa'a.

KARANTA WANNAN: Kakar wasanni ta Premier: Matasan 'yan wasa biyar masu tashe a taka leda

Wasu kuma daga cikin daliban sun bayyana cewa ziyartar kifin tana yaye mu su kunci da damuwa.

Da ya ke aika sakonsa na ta'aziyyar Mafish, shugaba Lungu ya yi amfani da kalmomin tsohon dan gwagwarmaya na kasar India, Mahatma Gandhi.

"Za a iya gane halin kasa da jama'arta ta hanyar lura da yadda suke mu'amala a tsakaninsu da dabbobi.

"Tabbas za mu yi kewarka, ka samu kyakyawan karshe," kamar yadda Lungu ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A nasa sakon, jagoran 'yan adawa, Hakainde Hichilema, cewa ya yi: "mu na mika sakon ta'aziyya ga daliban CBU, na baya da na yanzu, a kan mutuwar Mafish."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel