Pakistan ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aika sakon batanci ga Musulmi

Pakistan ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aika sakon batanci ga Musulmi

- Wata kotu da ke zama a Gabashin Pakistan, garin Lahore ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aikata laifin batanci

- Da ya ke jawabin kare kansa a gaban kotun, Pervaiz ya yi ikirarin cewa shugaban nasa a wajen aikin yana matsa masa akan ya koma Musulunci

- Doka mai tsauri ta Pakistan ta haramta batanci ta sanya hukuncin kisa ga wanda ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW), ko wani cin mutunci ga Musulunci

Wata kotu da ke zama a Gabashin Pakistan, garin Lahore ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aikata laifin batanci, a cewar lauyansa.

Hakan na daga cikin tsauraran matakan da Pakistan ta dauka kan cin zarafi ko batanci ga addinai, musamman marasa karfi.

Asif Pervaiz, (37) ya kasance a kulle tun 2013 a lokacin da aka zarge sa da tura sakonnin batanci ga shugabansa a wajen aiki, lauyansa Saif-Ul-Malook ya shaidawa Al Jazeera.

Kotun ta yi watsi da bayanan da ya gabatar na karyata dukkanin zarge zargen da ake yi masa, kuma kotun ta yanke masa hukuncin kisa a ranar Talata.

KARANTA WANNAN: Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta

Pakistan ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aika sakon batanci ga Musulmi
Pakistan ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aika sakon batanci ga Musulmi
Source: Twitter

"Shi wanda ake shari'ar da shi, shugaban Asif ne a inda ya ke aiki," a cewar Malook.

"Ya karyata dukkanin zarge zargen da ake yi masa, kuma ya ce mutumin yana kokarin mayar da shi addinin Musulunci ne."

Da ya ke jawabin kare kansa a gaban kotun, Pervaiz ya yi ikirarin cewa shugaban nasa a wajen aikin yana matsa masa akan ya koma Musulunci, kuma bai aikata laifin tura sakon batanci ba.

Muhammad Saeed Khokher, wanda ake shari'ar da shi, ya karyata zargin Parvaiz, a cewar lauyan sa, Ghulam Mustafa Chaudhry.

Chaudhry ya ce akwai wasu ma'aikata Kiristoci karkashin shugaban, amma ba a taba kawo koken Khokher na yunkurin mayar da su Musulunci ba.

Doka mai tsauri ta Pakistan ta haramta batanci ta sanya hukuncin kisa ga wanda ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW), ko wani cin mutunci ga Musulunci, ko Al-Qur'ani ko muhimman mutane.

KARANTA WANNAN: Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gwangwaje Bashir Maishadda da sabuwar mota

A halin yanzu, akwai mutane kusan 80 a kurkukun Pakistan bisa kama su da laifin batanci, inda rabinsu suna fuskantar hukuncin kisa, a cewar hukumar 'yancin addinai ta Amurka (USCIRF).

A wani labarin; Rikici ya kaure tsakanin Abraham Musonda (52) da matarsa mai shekaru 40, sakamakon gaza cire mata bera da ta gani a kusa da gadonta, a gidansu da ke garin Kitwe, kasar Zimbabwe.

A tsakiyar rikicin ne, matar mai suna Mukupa ta fusata, ta sa hakori ta gutsirewa mijin na ta mazakuta, saboda gaza cire mata beran, a cewar rundunar 'yan sanda.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa matar ta yi ikirarin beran yana takura mata tare da hanata rawan gaban hantsi, musamman lokacin da ta dawo daki ta same shi a gefen gadonta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel