Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta

Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta

- Rikici ya kaure tsakanin Abraham Musonda (52) da matarsa mai shekaru 40, sakamakon gaza cire mata bera da ta gani a kusa da gadonta

- A tsakiyar rikicin ne, matar mai suna Mukupa ta fusata, ta sa hakori ta gutsirewa mijin na ta mazakuta, saboda gaza cire mata beran

- A cewar jaridar Metro UK, an garzaya da Mr Musonda asibitin Kitwe, domin ba shi agajin gaggawa

Rikici ya kaure tsakanin Abraham Musonda (52) da matarsa mai shekaru 40, sakamakon gaza cire mata bera da ta gani a kusa da gadonta, a gidansu da ke garin Kitwe, kasar Zimbabwe.

A tsakiyar rikicin ne, matar mai suna Mukupa ta fusata, ta sa hakori ta gutsirewa mijin na ta mazakuta, saboda gaza cire mata beran, a cewar rundunar 'yan sanda.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa matar ta yi ikirarin beran yana takura mata tare da hanata rawan gaban hantsi, musamman lokacin da ta dawo daki ta same shi a gefen gadonta.

KARANTA WANNAN: Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gwangwaje Bashir Maishadda da sabuwar mota

Duk wani kokarinta na yin bacci a wannan dare ya gagara, sakamakon guje gujen da beran ke yi a cikin dakin, lamarin da ya tilasta ta kiran mijin nata, don ya fitar da shi, a cewar ta.

Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta
Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta
Source: Depositphotos

Amma da mijin ya ki amincewa da wannan bukata, sai Mukupa ta samu damar kafa hakoranta a mazakutarsa, lamarin da ya jawo ya samu rauni mai muni.

Bothwell Namuswa, mataimakin kwamishinan 'yan sanda na shiyyar Copperbelt, ya shaidawa manema labarai cewa ma'auratan sun rabu, amma suna zama a gida daya, daki daban daban.

A cewar jaridar Metro UK, an garzaya da Mr Musonda asibitin Kitwe, domin ba shi agajin gaggawa kan wannan mummunan al'amari.

A wani labarin makamancin wannan, 'yan sanda a kasar sun cafke wani mutum da ya duki yaron budurwarsa, har ya tsinke masa mazakuta da kunbarsa.

KARANTA WANNAN: 'Yadda muka kashe wasu masu jego, kuma muka yi awon gaba da jariransu'

Mohammad Mahmoud Shaar, na yankin Coconut Creek, Florida, ya ajiye budurwasa a wajen aikinta a ranar Alhamis, kana ya dauki yaronta mai shekaru hudu ya kaishi gidan raino.

Shaar sai ya farmaki yaron a lokacin da ran sa ya baci bayan da mahaifiyar yaron ta sauka daga motar, a cewar rahoton cafke mutumin.

Ofishin 'yan sandan Sheriff na yankin Broward ya ce gidan rainon na da tazarar mil 1.6 daga wajen aikin mahaifiyar, amma sai da Shaar ya kwashe mintuna 20 kafin ya isa.

Mai rainon yaron ta ce taga yaron yana kuka cikin firgici, kuma Shaar ya ajiye shi ba tare da ya yi mata bayanin abunda ya faru ba, ya yi tafiyarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel