Da duminsa: Buhari zai kaddamar da shirin tallafawa 'yan kasuwa da N50,000 a kowanne wata

Da duminsa: Buhari zai kaddamar da shirin tallafawa 'yan kasuwa da N50,000 a kowanne wata

- Shugaba Buhari, ya sanar da cewa, gwamnatin sa ta shirya kaddamar da gidauniyar tallafawa matsakaitu da kananan 'yan kasuwa a Nigeria

- A wannan sabon shirin, gwamnati za ta dinga tallafawa 'yan kasuwar ne da N50,000 a kowanne wata

- Haka zalika, babban bankin ya fitar da tiriliyan daya, don tallafawa bangaren masana'antun kere kere, inda tuni aka raba N191bn daga cikin kudin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya sanar da cewa, gwamnatin sa ta shirya kaddamar da wata gidauniyar tallafawa matsakaitu da kananan 'yan kasuwa a Nigeria.

A wannan sabon shirin, a cewar shugaba Buhari, gwamnati za ta dinga tallafawa 'yan kasuwar ne da N50,000 a kowanne wata.

Sai dai, gwamnati za ta dauki tsauraran matakai wajen zakulo 'yan kasuwan da za su ci moriyar wannan tallafi, kuma 'yan kasuwar za su fito daga kowanne fanni na kasuwanci.

Haka zalika, shugaban kasar ya ce a yunkurin gwamnatinsa na farfado da tattalin arziki, a farkon shekarar 2020, babban bankin Nigeria ya fitar da N100bn don tallafawa masana'antu.

A cikin N100bn na tallafin, an rabawa kamfanonin kiwon lafiya da sarrafa magunguna, wanda tuni aka kaddamar da shirye shirye 37, akan kudi N37bn.

KARANTA WANNAN: Duniya labari: An kama magidanci yana lalata da yar shekaru 4 cikin Masallaci a Bauchi

Da duminsa: Buhari zai kaddamar da shirin tallafawa 'yan kasuwa da N50,000 a kowanne wata
Da duminsa: Buhari zai kaddamar da shirin tallafawa 'yan kasuwa da N50,000 a kowanne wata
Asali: Facebook

Haka zalika, babban bankin ya fitar da tiriliyan daya, don tallafawa bangaren masana'antun kere kere, inda tuni aka raba N191bn daga cikin kudin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a wani taron nazarin ayyukan da ma'aikatu suka gudanar na shekarar farko, wanda aka gudanar a fadar shugaban kasar.

Mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar kafofin sadarwa na zamani, Mr Tolu Ogunlesi ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na Twitter.

Daga cikin mahalarta taron, akwai ministoci, shuwagabannin hukumomi da sashe-sashe, manyan jami'an gwamnati da kuma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya jagoranci zaman a madadin shugaban kasa.

Idan ba a manta ba, a lokacin da ministoci suka kama aiki a shekarar da ta gabata, fadar shugaban kasa ta basu jaddawalin ayyukan da za su gudanar.

A lokacin, ministoci da manyan sakatarorin ma'aikatunsu ne suka sa hannu a kundin ayyukan, kana suka isar da sakon haka ga shuwagabannin sashe sashe da ke karkashinsu.

KARANTA WANNAN: FG ta haramtawa wasu kamfanonin jiragen sama na waje aiki a Nigeria

A jawabinsa na bude taro, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce a tsakanin 18 ga watan Disamba 2019 zuwa 22 ga watan Yuli 2020, dukkan ma'aikatu sun gabatar da rahoton ayyukansu ga majalisar zartaswar kasar.

A cikin rahoton, sun zayyana ayyukan da suka gudanar kamar yadda ya ke kunshe a cikin jaddawalin ayyukan da aka basu, da kuma wadanda ba su samu damar yi ba.

A wani labarin; Gwamnatin tarayya ta saki sunayen wasu kamfanonin jiragen sama na kasar waje da ta haramtawa aiki a Nigeria, yayin da aka fara jigilar mutane a makon da ya gabata.

Kamfanonin jiragen sama na kasar waje da aka haramtawa aiki a kasar a cewar ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, sun hada da Air France, KLM, da Etihad.

Sauran kamfanonin sun hada da Rwandair, Lufthansa, TAAG Angola Airlines da sauransu. Wasu kuma daga cikin kamfanonin da aka haramtawa aikin, anyi hakan ne saboda kasashensu ba su amince su fara aiki a can ba.

Ire iren wadannan kamfanonin sun hada da Caper Verde da kuma South African Airlines.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel