Tashin hankali: Mai gadi ya yiwa amarya kisan gilla ya binne gawarta ya gudu da motarta

Tashin hankali: Mai gadi ya yiwa amarya kisan gilla ya binne gawarta ya gudu da motarta

- An kama wani mai gadi da ya kashe wata budurwa dake shirin zama amarya ya binne gawarta

- Mai gadin an kama shi yana tuka daya daga cikin motocin budurwar ne tare da matarshi da 'ya'yanshi a ciki

- Haka kuma an kama daraktan fim din kamfanin Nollywood dake zaune da budurwar gida daya za a bincike shi

An gano wani saurayin mai gadi da ya kashe wata amarya mai shekaru 35 a duniya da ake shirin daura mata aure ya binne gawarta ba tare da kowa ya sani ba.

Budurwar mai suna Joy Obiageli Onakanse ta bata mako biyu da suka gabata. Da 'yan uwanta suka kasa samun damar tuntubar ta, sun kai rahoto ga ofishin 'yan sanda akan batan ta.

An gano mai gadin gidan da Ms Joy take zama yana tuka motarta tare da matarshi da 'ya'yanshi a ciki, bayan gabatar da bincike. Bayan tsananta bincike an gano ramin da mutumin yayi ya binne ta a ciki.

Tashin hankali: Mai gadi ya yiwa amarya kisan gilla ya binne gawarta
Tashin hankali: Mai gadi ya yiwa amarya kisan gilla ya binne gawarta
Source: Facebook

Mai gadin mai suna Isaac Sunday wanda ya fito daga jihar Neja, an kama shi. Haka kuma wani daraktan fina-finan kudancin Najeriya na Nollywood, Nonso Ekene, daga jihar Anambra shima an kama shi, bayan an gano cewa yana zaune a gida daya da ita, kuma ana zargin shi da hannu a lamarin.

Ya zuwa yanzu dai suna hannun hukumar 'yan sanda ana gabatar da bincike a kansu domin gano gaskiyar lamarin kafin a mika su gaban kotu don yanke musu hukunci kamar yadda doka ta tanada.

KU KARANTA: Mutumin da wani magidanci ya kira su taru su ladabtar da danshi ya cakawa yaron wuka

A wani labari makamancin haka kuma, Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta kama wata budurwa mai shekaru 25, mai suna Oyinye Chime, wacce ke dauke da ciki, da laifin cakawa saurayinta mai suna Eleyi Azubuike wuka, inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar shi a gidanshi dake Ochiagha dake Nkpor, a cikin jihar ranar Laraba 2 ga watan Satumba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Muhammed Haruna, wanda ya bayyana haka ga manema labarai, ya ce 'yan sandan sun karbi rahoton kisan, suka kuma yi gaggawar kai ziyara wajen da lamarin ya faru a ranar Laraba din.

"Bincike ya nuna cewa marigayin ya yiwa budurwar ciki, sai ya bukaci a zubar da cikin, sai taki yadda, ita ma ta bukaci ya bata kudi da za ta kula da yaron, sai shima yaki yadda. Hakan yayi sanadiyyar rikici ya barke tsakanin masoyan har yayi sanadiyyar mutuwar marigayin."

A cewar Haruna, 'yan sanda dake aiki a ofishin dake Ogidi, tare da shugabancin DPO CSP Ekuri Remigius, sun kai ziyara wajen da lamarin ya faru inda suka yi gaggawar garzayawa da marigayin asibitin Enu Mission dake Ogidi domin ceto rayuwar shi, inda a asibitin ne aka tabbatar da cewa ya mutu. Budurwa ta kashe saurayin da yayi mata ciki, bayan ta bukaci ya biyata kudi ya ki

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel