Yanzu-yanzu: FG ta haramtawa wasu kamfanonin jiragen sama na waje aiki a Nigeria

Yanzu-yanzu: FG ta haramtawa wasu kamfanonin jiragen sama na waje aiki a Nigeria

Rahotanni na nuni da cewa, Gwamnatin tarayya ta saki sunayen wasu kamfanonin jiragen sama na kasar waje da ta haramtawa aiki a Nigeria, yayin da za a fara jigilar mutane ranar Asabar.

Kamfanonin jiragen sama na kasar waje da aka haramtawa aiki a kasar a cewar ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, sun hada da Air France, KLM, da Etihad.

Sauran kamfanonin sun hada da Rwandair, Lufthansa, TAAG Angola Airlines da sauransu.

Wasu kuma daga cikin kamfanonin da aka haramtawa aikin, anyi hakan ne saboda kasashensu ba su amince su fara aiki a can ba.

Ire iren wadannan kamfanonin sun hada da Caper Verde da kuma South African Airlines.

KARANTA WANNAN: Duniya labari: An kama magidanci yana lalata da yar shekaru 4 cikin Masallaci a Bauchi

Yanzu-yanzu: FG ta haramtawa wasu kamfanonin jiragen sama na waje aiki a Nigeria
Yanzu-yanzu: FG ta haramtawa wasu kamfanonin jiragen sama na waje aiki a Nigeria
Source: UGC

Kamfanonin jiragen da aka baiwa lasisin gudanar da ayyukansu a kasar sun hada da: Middle-East, British Airways, Delta airlines, Qatar Airways, da Ethiopian Airlines.

Sauran sun hada da; Egyptair, Air Peace, Vir'gin Atlantic, Asky, Africa World Airways (AWA), Air Cote-d’Ivoire, Kenya Airways, Emirate, da kuma Turkish airlines.

Ana sa ran dukkanin kamfanonin za su bi matakan kariya daga kamuwa da cutar COVID-19.

Da ya ke bayyana hakan a Abuja a ranar Alhamis, Sirika, ya kuma bayar da jerin dokoki ga fasinjojin da zasu shigo kasar da kuma wadanda zasu fita.

Cikakken labarin yana zuwa...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel