Mutumin da wani magidanci ya kira su taru su ladabtar da danshi ya cakawa yaron wuka

Mutumin da wani magidanci ya kira su taru su ladabtar da danshi ya cakawa yaron wuka

Wani mutumi da wani magidanci ya kira domin ya taya shi ladabtar da danshi da yake sata yaki dainawa ya zaro wuka ya cakawa dan ya fadi ya mutu, saboda yaron yaki bayar da hadin kai

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kama wani mai suna Felix Ezike, mai shekaru 27, da laifin cakawa wani matashi dan shekara 19 mai suna Deji Animashaun wuka, inda tayi sanadiyyar mutuwar shi a yankin Egbe dake Ikotun, cikin jihar Legas.

A cewar rahoton 'yan sandan, mahaifin Deji, Dada Animashaun, ya gayyaci Felix gidanshi domin ya taimaka masa wajen ladabtar da danshi wanda aka kama yana sata kuma yaki canja halinshi.

Mutumin da wani magidanci ya kira su taru su ladabtar da danshi ya cakawa yaron wuka
Mutumin da wani magidanci ya kira su taru su ladabtar da danshi ya cakawa yaron wuka
Asali: UGC

An ruwaito cewa Deji yaki bayar da hadin kai lokacin da Felix yayi kokarin ladabtar dashi. Felix ranshi ya baci sai ya fito da wuka, inda yayi amfani da ita wajen cakawa Deji a kanshi da kuma jikinshi.

Cikin gaggawa mahaifin Deji ya garzaya da dan asibiti, inda ya mutu a asibitin lokacin da ake masa magani.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Bala Elkana, ya ce:

KU KARANTA: Budurwa ta kashe saurayin da yayi mata ciki, bayan ta bukaci ya biyata kudi ya ki

"A ranar 28 ga watan Agusta, 2020, da misalin karfe 4:30 na yamma, Dada Animashaun, dake kan layin Rasheed Bello, Egbe, Ikotun, ya gayyaci wani mai suna Felix Ezike, mai shekaru 27, zuwa gidan shi domin ya taya shi ladabtar da danshi mai suna Deji Animashaun, mai shekaru 19, saboda satar da yake yi kuma yaki dainawa.

"A kokarin da yake na kare kanshi daga hukuncin da ake yi masa, sai ji yayi an caka masa wuka a kai da jikinsa. A wurin yaron ya fadi, inda aka garzaya dashi asibiti domin ceto rayuwar shi, a lokacin ne ya mutu. Jami'an mu sun ziyarci wajen da lamarin ya faru suka dauke gawar zuwa wajen ajiye gawa dake asibitin Yaba," ya ce.

Bala ya kara da cewa duka da uban yaron da kuma Felix suna hannunsu. Ya ce a yanzu haka suna gabatar da bincike akan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel