Farawa da iyawa: Dakarun tsaron Amotekun na jihar Ondo sun cafke masu garkuwa guda uku

Farawa da iyawa: Dakarun tsaron Amotekun na jihar Ondo sun cafke masu garkuwa guda uku

- Dakarun kungiyar tsaron Amotekun, jihar Ondo, sun samu nasarar cafke wasu gawurtattun masu garkuwa da mutane guda uku

- An cafke mutanen uku bayan da suka yi garkuwa da shahararren dan kasuwar nan, Mr Kunle Agbayewa

- Rahotanni sun bayyana cewa mazauna yankin ne suka kokawa dakarun Amotekun, inda su kuma suka bazama neman mutanen, har suka kamasu

Dakarun kungiyar tsaron Amotekun, jihar Ondo, sun samu nasarar cafke wasu gawurtattun masu garkuwa da mutane guda uku, da suka addabin yankin Owo/Ose a jihar.

An cafke mutanen uku bayan da suka yi garkuwa da shahararren dan kasuwar nan, Mr Kunle Agbayewa a Idoani, karamar hukumar Ose, a ranar Laraba.

Yan ta'addan sun farmaki kamfanin da ofishinsa ya ke, suka yi awon gaba da shi, awanni 24 bayan da aka yi garkuwa da shugaban babban asibitin Idoani, Mr Olufemi Adeogun.

An yi garkuwa da shugaban asibitin ne tare da wasu ma'aikatan kiwon lafiya guda biyu. Kuma duka akan hanya daya ce da kamfanin da aka sace dan kasuwar.

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna yankin ne suka kokawa dakarun Amotekun, inda su kuma suka bazama neman mutanen, har suka kamasu, tare da ceto wadanda aka sace.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Oyo ta janye dokar hana zirga zirga, ta ce kowa ya wala

Farawa da iyawa: Dakarun tsaron Amotekun na jihar Ondo sun cafke masu garkuwa guda uku
Farawa da iyawa: Dakarun tsaron Amotekun na jihar Ondo sun cafke masu garkuwa guda uku
Asali: UGC

Da ya ke tabbatar da kama masu garkuwan, shugaban rundunar Amotekun na jihar, Adetunji Adeleye, ya ce sun ceto wadanda aka sace, tare da kama yan ta'addan.

Ya ce jami'ansa sun cafke masu garkuwa da mutanen, sun mika su ga rundunar 'yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma yanke masu hukunci.

A wani labarin; Kwamitin yaki da cutar COVID-19 a jihar Oyo, karkashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde, ta sanar da janye dokar hana zirga zirga daga karfe 10 na dare da aka kakaba a fadin jihar.

Sanarwa daga babban sakataren watsa labarai na gwamnan, Mr Taiwo Adisa, wacce ke dauke da rahoton zaman kwamitin na ranar 31 ga Agusta, ya ce an janye dokar ne bayan dogon nazari.

Sai dai kwamitin ya gargadi gidan rawar dare da su kauracewa cunkusa mutane a matsattsun wurare, kasancewar bincike ya nuna cutar tafi yaduwa a cunkuson jama'a.

A cewar sanarwar, za a tura da takardar bayanan kariya ga mamallakan gidajen rawar dare, ta hannun cibiyar aikin gaggawa (EOC), don gargadarsu akan barin baki barkatai a gidajensu.

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa kwamitin ya gargadi al'ummar jihar da su ci gaba da bin dokokin yaki da yaduwar COVID-19, kasancewar har yanzu cutar ba ta tafi gaba daya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng