Sakamakon kamuwa da COVID-19: Wani babban likita a Kaduna ya mutu

Sakamakon kamuwa da COVID-19: Wani babban likita a Kaduna ya mutu

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu daga jaridar The Cable, na nuni da cewa Dr. Clement Bakam, wani babban likita a jihar Kaduna, ya mutu sakamakon kamuwa da annobar mashako, wato Covid-19.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba daga Abdulsalam Abdulrazak, jami'in hulda da jama'a na kungiyar likitoci (NMA) reshen Kaduna, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin.

Abdulrazak ya ce kafin mutuwarsa, marigayi Bakam shine shugaban shirin cibiyar rigakafi ta jihar Kaduna (KadSERICC).

"A madadin shugaban kungiya, ina mai alhinin sanar da ku rasuwar abokin aikinmu, Dr Clement Bakam, biyo bayan fama da rashin lafiya ta COVID-19," a cewar jami'in.

"Kafin mutuwarsa, marigayi Bakam shine shugaban shirin cibiyar rigakafi ta jihar Kaduna (KadSERICC).

KARANTA WANNAN: Na damu kwarai da yadda farashin kayan abinci ke tashi, amma a kara hakuri - Buhari

Sakamakon kamuwa da COVID-19: Wani babban likita a Kaduna ya mutu
Sakamakon kamuwa da COVID-19: Wani babban likita a Kaduna ya mutu
Asali: UGC

"Muna mika sakon ta'aziyyarmu ga iyalan mamacin, abokansa, abokan aikinsa da kuma ARD Kaduna. Allah ya bamu hakurin jure rashinsa gaba daya."

Ya zuwa yanzu, jihar Kaduna ta samu mutane 2,163 da suka kamu da cutar a fadin jihar.

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 216 a fadin Najeriya.

Kwana takwas a jere yanzu jihar Plateau na zarce Legas da Abuja wajen yawan adadin sabbon wadanda suka kamu da cutar.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Laraba 2 ga Satumba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 216 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Plateau-59

Rivers-27

Abia-22

Lagos-20

Oyo-18

Enugu-17

Kaduna-11

FCT-11

Ogun-10

Ebonyi-4

Osun-4

Ekiti-4

Delta-3

Edo-3

Akwa

Ibom-2

Bauchi-1

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel