Niger: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 9 sun bakaci N10m kudin fansa

Niger: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 9 sun bakaci N10m kudin fansa

- Yan bindiga sun kai farmaki a kasuwar Kusasu da ke cikin karamar hukumar Shiroro, jihar Niger kuma sun yi awon gaba da mutane tara

- Bayan kwanaki uku, 'yan bindigar sun tuntubi iyalan wadanda suka yi garkuwa da su, inda suka bukaci N10m a matsayin kudin fansa

- Tuni dai rundunar 'yan sanda ta cafke wasu mutane biyar da ake zargin masu leken asirin 'yan bindigar ne

Yan bindiga sun kai farmaki a kasuwar Kusasu da ke cikin karamar hukumar Shiroro, jihar Niger kuma sun yi awon gaba da mutane tara. Lamarin ya faru ne a ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun shiga kasuwar ne domin diban kayan abinci da sauran kayan bukatun su, inda suka kare da yin garkuwa da mutane tara.

Wakilin jaridar Vanguard ya ruwaito cewa 'yan bindigar sun shiga kasuwar ne da tsakiyar rana, haye a saman babura sama da 15, kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Yan bindigar a cewar wata majiya mai tushe, sun tuntubi iyalan wadanda suka yi garkuwa da su bayan kwanaki uku, sun bukaci N10m a matsayin kudin fansar mutanen.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga na can suna cin karensu ba babbaka a Kagara, jihar Niger

Niger: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 9 sun bakaci N10m kudin fansa
Niger: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 9 sun bakaci N10m kudin fansa
Source: Twitter

Rahotanni sun yi nuni da cewa 'yan garin ba su da masaniyar cewa da 'yan bindigar suke cinikayya, har sai da suka kai masu farmakin, lamarin da ya basu tsoro.

Tuni dai rundunar 'yan sanda ta cafke wasu mutane biyar da ake zargin masu leken asirin 'yan bindigar ne, kuma sun kaddamar da neman mutane takwas 'yan Shiroro.

Haka zalika, an cafke wasu 'yan bindigar guda biyu a kasuwar Zumba a karamar hukumar Shiroro, kuma an kamasu da bindiga kirar AK-47.

Biyo bayan matsin lamba daga rundunar 'yan sanda, ta'addancin 'yan bindigar ya ragu a yankin, har sai bayan garkuwa da wasu ma'aika biyu da kashe sojoji uku.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar, ASP Wasiu Abiodun, ya ci tura, sai dai wata majiya mai tushe ta tabbatar da labarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel