Ko gwamnati ta bayar da umurni, mu ba zamu bude makarantu ba - Kungiyar malamai

Ko gwamnati ta bayar da umurni, mu ba zamu bude makarantu ba - Kungiyar malamai

- Malamai a jihar Imo sun ce ba za su bude makarantun Firamare da Sakandire ba ko da gwamnatin jihar ta bayar da umurnin hakan

- Shugaban kungiyar NUT na jihar, Philip Nwanshi ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a Owerri

- Akalla malamai 2000 ne suke bin bashin albashi da sauran hakkokinsu na kusan watanni bakwai

Malamai a jihar Imo sun ce ba za su bude makarantun Firamare da Sakandire ba ko da kuwa gwamnatin jihar ta bayar da umurnin bude makarantun, a wannan yanayi na COVID-19.

Shugaban kungiyar NUT na jihar, Philip Nwanshi ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a Owerri, cewa har yanzu gwamnatin jihar ba ta cika alkawarin da ta daukar masu ba.

A cewar Nwanshi, a watannin da suka wuce, sun hadu da gwamna Hope Uzodimma ya sha alwashin biyan basussukan albashin da ake bin malaman, sai dai shiru har yanzu.

KARANTA WANNAN: Obaseki, Ize-Iyamu da Oshiomhole sun shiga ganawar gaggawa

Ko gwamnati ta bayar da umurni, mu ba zamu bude makarantu ba - Kungiyar malamai
Ko gwamnati ta bayar da umurni, mu ba zamu bude makarantu ba - Kungiyar malamai
Source: Twitter

Akalla malamai 2000 ne suke bin bashin albashi da sauran hakkokinsu na kusan watanni bakwai.

"A karamar hukumar Ngor Okpala, babu makarantar firamare da ta samu albashi tun daga watan Maris har yanzu na wannan shekarar. A Owerri ta Yamma da sauransu, nan ma haka ne.

"Babu ta yadda zaka fada mun cewa wai matsalar BVN da bankunansu ne ta sa aka rike masu albashi. Ba zaka ce mun takardun duk malaman matsala daya bace," cewar sa.

Ya jaddada cewa malamai a jihar ba zasu koma karatu ba ko da kuwa gwamnatin jihar ta bude makarantun, har sai an biya basussukan albashin da malaman ke bi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel