Subhanallah: Jaridar Charlie Hebdo ta sake buga hotunan batanci ga Annabi Muhammadu (SAW)

Subhanallah: Jaridar Charlie Hebdo ta sake buga hotunan batanci ga Annabi Muhammadu (SAW)

Domin tunawa da makon da aka kai hari ga jaridar Charlie Hebdo a 2015, jaridar kasar Faransan, ta sake wallafa hotunan barkwancin da suka yi shekaru 5 da suka wuce, na batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

A 2015, jaridar wacce tayi kaurin suna wajen yin zane zanen barkwanci, ta zana siffar Annabi, lamarin da ya fusata kungiyar wasu Musulmai, har suka kai mata hari.

A shekarar 2005 ne jaridar Jyllands-Posten ta fara wallafa zanen.

Sake wallafa zanen na zuwa ne kwana ɗaya kafin soma shari'ar mutanen nan 14 da ake zargi da taimaka wa wasu mutum biyu masu iƙirarin jihadi da kai harin bindiga a ofishin mujallar a ranar 7 ga watan Janairun 2015.

A wannan karon, shugaban dab'i na jaridar, Laurent "Riss" Sourisseau ya ce ba za su ja da baya ba, kuma tuni sun saki hotunan a yanar gizo, ba zasu wallafa a jaridu ba.

KARANTA WANNAN: Tirela ta bi ta kan motar Adam Oshiomole, mutane da yawa sun mutu

Subhanallah: Jaridar Charlie Hebdo ta sake buga hotunan batanci ga Annabi Muhammadu (SAW)
Subhanallah: Jaridar Charlie Hebdo ta sake buga hotunan batanci ga Annabi Muhammadu (SAW)
Asali: Twitter

Riss ya rasa hannunsa na dama a harin da aka kaiwa jaridar a ranar 7 ga watan Janairu, sai dai ya rayu ne bayan da ya yi lambo kamar ya mutu a lokacin.

Hotunan barkwancin da suka zana akan Annabi Muhammadu, sun zamo abun batanci da cin zarafi, wanda ya sa har kungiyar Said da Cherif Kouachi suka farmaki ginin jaridar.

A harin, mutane 12 ne suka rasa rayukansu.

Wadannan hare haren su ne mafarin kai hare haren masu ikirarin jihadi a fadin Faransa.

Shafin farko na mujallar na ɗauke da zanen barkwanci har guda 12 na Annabi Muhammad S.A.W, waɗanda aka wallafa a wata jaridar harshen Danish kafin aka wallafa su a mujallar Charlie Hebdo.

Daya daga cikin zanen barkwancin ya nuna Annabi Muhammad S.A.W sanye da bam a kansa a maimakon rawani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel