Kyauta kasar China za ta gina jami'ar sufuri da za ta ci $50m a Daura - Minista

Kyauta kasar China za ta gina jami'ar sufuri da za ta ci $50m a Daura - Minista

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa a kyauta gwamnatin kasar China za ta gina jami'ar sufuri ta Daura, wacce za ta lashe $50m

- Ya kuma sanar da cewa cewa tawagar kwararrun masu zane, mashawarta kan aikin, sun sha alwashin gudanar da ayyukansu a kyauta

- Ministan ya kara da cewa aikin zai kuma hada da gina makarantun Firamare da Sakandire a cikin harabar jami'ar

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa a kyauta gwamnatin kasar China za ta gina jami'ar sufuri ta Daura, wacce za ta lashe $50m, da za a kammala gininta a Satumbar 2021.

Ministan ya bayyana hakan a karshen makon da ya gabata a Daura, jihar Katsina, lokacin ziyarar yadda aikin yake gudana.

Ya kuma sanar da cewa cewa tawagar kwararrun masu zane, mashawarta kan aikin, sun sha alwashin gudanar da ayyukansu a kyauta ba tare da karbar sisin kwabo ba.

Ministan sufurin, ya kuma bayyana cewa dalilin samar da jami'ar sufurin shine gudanar da fannin sufurin jiragen kasa wanda kamfanin gine gine na China (CCECC) ya ke kan ginawa.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Lagos ta karyata jita-jitar bude makarantu a watan Satumba

Kyauta kasar China za ta gina jami'ar sufuri a kan $50m a Daura - Minista
Kyauta kasar China za ta gina jami'ar sufuri a kan $50m a Daura - Minista
Asali: Twitter

Ya ce yi hasashen cewa za a kammala ginin jami'ar a cikin watan Satumbar 2021.

Ministan ya kara da cewa aikin zai kuma hada da gina makarantun Firamare da Sakandire a cikin harabar jami'ar.

"Akwai maganganu da yawa na cewar su kamfanin CCECC ba su fara gina komai ba. Amma da muka zo sai muka taras suna aikinsu. Yanzu ne suka samu amincewa daga gwamnatin jihar."

Ya kara da cewa, "Za a fara zunzurutun ginin ne a watan Satumba kuma muna sa ran kammala ginin a cikin watan Satumbar shekara mai zuwa.

"Wannan ba ginin layin dogo bane. Wannan kyauta ce daga kamfanin CCECC. Ina da hasashen cewa zasu kammala ginin a watan Satumbar shekara mai zuwa.

"Akwai kudurin gina makarantar Firamare a ciki, musamman saboda malaman da suka zo daga wasu jihohi. Za a gina makarantu firamare da sakandire a cikin jami'ar.

"Kar ku manta, wannan aiki kyauta ne, don haka ba lallai bane su jajurce wajen yin aikin kamar yadda zasu yi idan kudi aka biya su ba."

Amechi ya kuma ce 'yan kwangilar sun sha alwashin baiwa aikin muhimmanci kamar yadda suka baiwa na ginin layin dogon.

Dangane da mutanen da ake bukata su gudanar da aikin, ministan ya ce kamfanin Chinan zai bayar da gudunmowarsa na shekaru 5, kafin gwamnatin tarayya ta samar da nata ma'aikatan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel