Da duminsa: Gwamnatin Lagos ta karyata jita-jitar bude makarantu a watan Satumba

Da duminsa: Gwamnatin Lagos ta karyata jita-jitar bude makarantu a watan Satumba

- Gwamnatin jihar Lagos ta karyata jita-jitar bude makarantu a watan Satumba

- Sashen OEQA, na ma'aikatar ilimi ta jihar Lagos ya ce wannan kalandar bude makarantun ba ta fito daga ofishinsu ba

- A makon da ya gabata ne a ka fara yada jita jitar cewa Lagos za ta bude makarantu daga ranar 21 ga watan Satumba 2020

Sashen tabbatar da nagartaccen ilimi, na ma'aikatar ilimin jihar Lagos, ya gargadi jama'a da su yi watsi da jita jitar da ake yadawa na cewar za a bude makarantun Lagos a watan Satumba.

Jita jitar ta kuma nuna cewa za a fara zangon karatu na biyu a ranar 11 ga watan Janairu 2021, a kammala a ranar 3 ga watan Mayu 2021.

Cikin wata sanarwa da ake yadawa kan bude makarantun jihar, an bukaci ma'aikatar ilimi, kimiyya da fasaha da masu ruwa da tsaki da su yi amfani da lokutan bude makarantun.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kaduna ta yi magana a kan bacewar barden Kwankwasiyya, Dadiyata

Da duminsa: Gwamnatin Lagos ta karyata jita-jitar bude makarantu a watan Satumba
Da duminsa: Gwamnatin Lagos ta karyata jita-jitar bude makarantu a watan Satumba
Asali: Twitter

Sai dai, a cikin wata sanarwa daga jami'in hulda da jama'a na sashen OEQA, Mr. Emmanuel Olaniran, ya ce wannan sanarwar bude makarantun ba ta fito daga ofishinsu ba.

"Muna sanar da jama'a cewa ofishinmu na OEQA bai fitar da kalandar bude makarantun sakandire ko na gaba da sakandire a jihar ba, a kaucewa wannan jita jitar,".

Wani abu da ya kamata ya nuna cewa kalandar da ake yadawa ta bogi ce, shine an kira sunan sashen da ma'aikatar ilimi da kuma kimiya da fasaha, wanda ba haka bane.

Ma'aikatar ilimi ta jihar Lagos ta sha bamban da ma'aikatar kimiyya da fasaha, kowacce ma'aikata na gudanar da aikinta na kashin kanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng