Da duminsa: Buhari ya rantsar da kwamitin tuntuba na majalisun dokoki da tarayya

Da duminsa: Buhari ya rantsar da kwamitin tuntuba na majalisun dokoki da tarayya

- Shugaba Buhari ya kaddamar da kwamitin tuntuba da neman maslaha na jam'iyyar APC a matakin kasa da jihohi

- Kwamitin zai kasance karkashin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbanjo

- Aikin kwamitin shine tuntubar bangaren majalisar zartarwa da na majalisar dokokin kasa domin inganta alakar aiki a tsakaninsu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya kaddamar da kwamitin tuntuba da neman maslaha na jam'iyyar APC a matakin kasa da jihohi.

Aikin kwamitin shine tuntubar bangaren majalisar zartarwa da na majalisar dokokin kasa domin inganta alakar aiki a tsakaninsu.

Da ya ke gabatar da jawabi a yayin taron, shugaba Buhari ya nuna takaicinsa kan yadda ake samun rikicin cikin gida, musamman a neman mukamai a cikin jam'iyyar.

Ya ce majalisar zartaswa na jiran ganin tsare tsare da shirye shiryen da wannan sabon kwamitin zai gabatarwa 'yan Nigeria.

Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da ke cikin kwamitin ba amma dai an san yana karkashin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbanjo.

An zabo mambobin kwamitin ne daga cikin shuwagabannin majalisar tarayya, shuwagabannin APC da kuma wakilai daga majalisar zartaswa.

KARANTA WANNAN: SERAP ta maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu

Buhari ya kaddamar da kwamitin tuntuba na jam'iyyar APC
Buhari ya kaddamar da kwamitin tuntuba na jam'iyyar APC
Source: UGC

Daga cikin mahalarta taron akwai mataimakin shugaban kasa Osinbajo, shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawan, mataimakinsa, Ovie Omo-Agege, da kuma kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya gabatar da jawabi a taron kaddamar da kwamitin.

Sauran mahalarta taron sun hada da babban alkali na kasa, Abubakar Malami, da kuma mukaddashin shugaban jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, da kuma Ibrahim Gambari.

A jawabin bude taron, Boss Mustapha, ya ce kwamitin zai kawo dai daita a alakar da ke tsakanin majalisar zartaswa da kuma majalisar tarayya.

Kyakkyawar alakar bangarorin guda biyu zai taimakawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen cika alkawuran da ta daukarwa 'yan Nigeria.

A zantawarsa da manema labarai bayan kammala taron, shugaban majalisar dattijai Lawan, ya ce da majalisar tarayya da ta zartaswa ba zasu kara yarda da mutane da Buhari ke nadawa a mukamai ba, musamman masu wulakanta bangaren majalisar dokokin.

Ya bada tabbacin cewa hadin kan da aka kafa kwamitin tuntubar don samar da shi, zai tabbatar da cewa majalisun biyu zasu rinka yin magana da murya daya.

Sai dai, ya yi alkawarin cewa wannan dai daiton ba shi zai hana gudanar da binciken kwakwaf tare da yin adalci a ayyukan majalisar tarayyar ba, da ya shafi majalisar zartaswar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel