Da duminsa: Rikici ya barke a jam'iyyar PDP reshen Ekiti, jam'iyyar ta dare gida 2

Da duminsa: Rikici ya barke a jam'iyyar PDP reshen Ekiti, jam'iyyar ta dare gida 2

- Rikicin da ya mamaye jam'iyyar PDP reshen jihar Ekiti ya kara tsamari, jam'iyyar ta dare gida biyu a ranar Asabar

- Rashin jituwar da ta shiga tsakanin Sanata Biodun Olujimi da Mr Ayo Fayose ta zama sanadin rabewar jam'iyyar

- Hon. Bisi Kolawole ya zama shugaban jam'iyyar daga bangaren Fayose, amma a bangaren Olujimi, Hon. Kehinde Odebunmi ne shugaban jam'iyyar

Rikicin da ya mamaye jam'iyyar PDP reshen jihar Ekiti ya kara tsamari a ranar Asabar, sakamakon rabewar jam'iyyar gida biyu, inda kowanne bangare ya zabi shuwagabannin sa.

Jam'iyyar PDP ta kasance cikin rabuwar kai a 'yan kwanakin nan, sakamakon rashin jituwar da ta shiga tsakanin Sanata Biodun Olujimi da Mr Ayo Fayose.

Sanata Biodun dai ita ce mai wakiltar mazabar Ekiti ta Kudu a majalisar dattijai, yayin da Mr Ayo shine tsohon gwamnan jihar, lamarin da ya jawo rabuwar kai a jam'iyyar.

Rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa ne ya tilasta kwamitin shugabancin jam'iyyar na kasa (NWC) a kafa kwamitin rikon kwarya na mutane bakwai da zai jagoranci jam'iyyar a jihar.

Kwamitin rikon kwaryar na karkashin shugabancin tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattijai, Sanata Hosea Agboola.

KARANTA WANNAN: Bayan shekara daya: Tashar jiragen sama ta Enugu za ta dawo bakin aiki

Da duminsa: Rikici ya barke a jam'iyyar PDP reshen Ekiti, jam'iyyar ta dare gida 2
Da duminsa: Rikici ya barke a jam'iyyar PDP reshen Ekiti, jam'iyyar ta dare gida 2
Source: Twitter

A taron zaben jam'iyyar da aka gudanar a ranar Asabar, tsohon kwamishin muhalli na jihar, Hon. Bisi Kolawole ya samu nasarar zama shugaban jam'iyyar daga inuwar Fayose.

Sai dai, a bangaren Olujimi, itama ta fitar da tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Kehinde Odebunmi a matsayin shugaban jam'iyyar.

Tawagar Fayose ta gudanar da zabenta a kan idanun tsohon gwamnan jihar, Segun Oni, a ginin baki na Petim, da ke a gidan baki na Lotus, babban birnin jihar.

Fayose ya gargadi mambon jam'iyyar da su kauracewa rashin da'a da biirewa umurnin jam'iyya, yana mai cewa an zalunci PDP a zaben 2018, amma 2022 na nan zuwa don daukar fansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel