Bayan shekara daya: Tashar jiragen sama ta Enugu za ta dawo bakin aiki

Bayan shekara daya: Tashar jiragen sama ta Enugu za ta dawo bakin aiki

- Rahotanni sun bayyana cewa tuni aka kammala dukkanin wasu gyare gyare a babbar tashar jiragen sama ta Akanu Ibiam

- Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama, ya sanar da cewa a ranar 30 ga watan Agusta, 2020 ne za a bude tashar jiragen

- A watan Agusta, 2019 ne aka rufe tashar jiragen domin baiwa gwamnati damar gudanar da gyare gyare

Rahotanni sun bayyana cewa tuni aka kammala dukkanin wasu gyare gyare a babbar tashar jiragen sama ta Akanu Ibiam, mizanin da za a iya bude tashar a yanzu.

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, wanda ya isa tashar jiragen a ranar Asabar domin duba matakin da aikin yake, ya ce komai ya yi dai dai yanzu, za a iya fara jigilar mutane.

A watan Agusta, 2019 ne aka rufe tashar jiragen domin baiwa gwamnati damar gudanar da gyare gyare, musamman tituna da kuma wasu gine gine da ke cikin tashar.

Ministan ya sanar da cewa a ranar 30 ga watan Agusta, 2020 ne za a bude tashar jiragen domin fara jigilar mutane da kaya.

A yayin ziyarar gani da idon tare da wasu kososhin gwamnatin jihar Enugu, Sirika ya ce ya gamsu da matakin aiki, yanzu za a iya bude tashar.

KARANTA WANNAN: Daga haduwa da Buhari - Ngige ya bukaci a tsige wasu Sarakuna 12

Bayan shekara daya: Tashar jiragen sama ta Enugu za ta dawo bakin aiki
Bayan shekara daya: Tashar jiragen sama ta Enugu za ta dawo bakin aiki
Asali: UGC

Ya kuma ce jirginsa ne na farko da ya fara sauka a filin tashar tun bayan da aka fara aikin gyare gyaren tashar.

Shahararren dan kasuwa, Engr. Arthur Eze ya isa tashar jirgin tare da Ministan.

A wani labarin; Ministan kwadago da daukar aiki, Dr Chris Ngige, ya bukaci gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, da ya tsige Sarakuna 12 da suka ce Abuja ganin shugaba Buhari ba tare da amincewar gwamnatin jihar ba.

A cewar Dr Chris Ngige, Prince Arthur Eze, wanda ya jagoranci tawagar zuwa Abuja, ya kamata ya fuskanci hukunci mai tsanani na wannan dan waken zagayen.

Idan ba a manta ba mun ruwaito maku cewa Gwamna Obiano ya dakatar da Sarakuna 12 saboda saboda ziyarar da suka kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

Gwamnatin jihar na kallon wannan ziyara a matsayin barazana da kuma karya dokokin mataki mataki na mulki, musamman da suka kebantu da masarautun jihar.

Sai dai Ngige, a wayar tarho da manema labarai a ranar Asabar, ya ce ba dakatarwa ya kamata ayiwa Sarakunan ba, kawai a tsige su shine mafi dacewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel