Allahu akbar: Rundunar 'yan sanda ta yi babban rashin jami'inta a Katsina

Allahu akbar: Rundunar 'yan sanda ta yi babban rashin jami'inta a Katsina

Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, mai kula da sashe na 14 na rundunar a jihar Katsina, Rabiu Yusuf, ya rasu. Majiya ta tabbatar da cewa Yusuf ya rasu ne a safiyar ranar Asabar.

Mataimakin Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Rabiu Yusuf, ya rasu, bayan fama da rashin lafiya a wani asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja.

Duk da cewa babu wani cikakken bayani kan rashin lafiyar da ta kwantar da shi, a cewar shafin yanar gizo na WITHIN NIGERIA.

Sai dai jaridar Punch ta ce mai magana da yawun rundunar na jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya sanar da rasuwar Yusuf a daren ranar Asabar, ta dandalin WhatsApp.

Gambo ya rubuta cewa, "Ina sanar da rasuwar AIG mai kula da shiyya ta 14, Katsina, AIG Rabi'u Yusuf. Allah ya gafarta masa, Ya sa Aljanna Firdausi ce makomarsa."

Duk wani yunkuri na samun karin bayani daga Gambo a daren ranar Asabar ya ci tura.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun kashe mutane 2 tare da awon gaba da dan sanda

Allahu akbar: Rundunar 'yan sanda ta yi babban rashin jami'inta a Katsina
Allahu akbar: Rundunar 'yan sanda ta yi babban rashin jami'inta a Katsina
Asali: Twitter

AIG Yusuf na daga cikin wadanda aka karawa matsayi zuwa mukamin AIG kuma aka bashi shugabancin sashen rundunar na 14 da ke jihar Katsina.

Sai dai, har zuwa lokacin rasuwarsa, bai kama aiki a sabon ofishin nasa ba.

Kafin kara masa matsayi zuwa AIG, Yusuf ya rike mukamin kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano.

A wani labarin; A ranar Juma'a wasu 'yan bindiga suka afkawa garuruwan Mararraban Rido da Juji da ke a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyu.

Yan bindigar sun kashe mutane biyu a Juji, ya yin da suka afkawa garin Maraban Rido, inda suka yi awon gaba da mutane hudu ciki har da dan sanda, maras lafiya.

An shaidawa manema labarai cewa daga cikin wadanda aka sace a harin da suka kai, har da yarinya mai shekaru 14, jami'in NSCDC da kuma mai gadi.

Wata majiya ta shaida cewa 'yan bindigar sun fara kai harin ne a gidan shugaban kungiyar CAN reshen karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Rev. Elisha Abu kafin shiga wasu gidajen.

Elisha Abu ya tabbatar da harin, yana mai cewa 'yan bindigar sun fara kai farmaki a gidansa da misalin karfe 11:57 na daren ranar Alhamis, inda suka yi kokarin shiga gidan amma suka kasa.

Ya bayyana cewa bayan sun bar kofar gidansa ne sai suka shiga gidajen da ke makwaftaka da shi, inda suka tafi da "wani dan sanda maras lafiya, wanda ya zo daga wata jiha.

A garin Juji da ke makwaftaka da Maraban Rido kuwa, nan ma 'yan bindigar sun yi harbe harbe inda suka kashe mutane biyu.

Wadanda aka kashen, 'yan wani gari ne da suka zo kawo dauki. Yan bindigar sun fara kaddamar da harin nasu da misalin karfe 11 na dare har zuwa shigar ranar Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel