Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana kan fadowar jirgi mai ungulu a jihar Lagos

Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana kan fadowar jirgi mai ungulu a jihar Lagos

Rahotan da muke samu yanzu na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon jaje da ta'aziyya ga iyalan wadanda hatsarin jirgi mai saukar ungulu ya ritsa da su a jihar Lagos.

Hadimin shugaban kasar ta fuskar kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad a shafinsa na Twitter, ya sanar da sakon jajen, a ranar Juma'a, 28 ga watan Agusta 2020.

Shugaba Buhari ya ce: "ina jajantawa iyalai, 'yan uwa da abokan wadanda hatsarin jirgin Bell 206 na kamfanin Quorum ya ritsa da su a ranar Juma'a, a wani gini da ke Opebi, jihar Lagos."

Idan ba a manta ba, mun ruwaito maku cewa A ƙalla mutane uku sun riga mu gidan gaskiya sakamakon haɗarin da wani jirgi ma saukan ungulu ya yi a Legas ya faɗa wasu gidaje.

KARANTA WANNAN: Kwamishina ta yi murabus kan zargin karkatar da N300m a Kwara

Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana kan fadowar jirgi mai ungulu a jihar Lagos
Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana kan fadowar jirgi mai ungulu a jihar Lagos
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya faɗa a ginin cocin Salvation Army da ke Opebi a Legas kuma ya shafi wasu gidaje da ke kusa da cocin.

Duk da cewa a yanzu ba a tabbatar ko akwai mutanen da suka mutu cikin gidajen da jirgin ya faɗa ba, mutum ɗaya ne cikin hudu da ke jirgin aka gani.

Kalli fifan bidiyo:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel