Farfesa Wole Soyinka ya caccaki shugaba Buhari a kan shirin kirkirar wata sabuwar doka a Najeriya

Farfesa Wole Soyinka ya caccaki shugaba Buhari a kan shirin kirkirar wata sabuwar doka a Najeriya

Fitaccen marubucin litattafan adabin wasa da wakoki, Farfesa Wole Soyinka, ya yi watsi da yunkurin gwamnatin tarayya na kirkirar dokar mallake albarkatun cikin ruwa da na karkashin teku da ke fadin kasa.

A shekarar 2018 ne majalisa ta fara yin watsi da kudarin, amma sai gashi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sake gabatar da shi a cikin watan Yuli na shekarar 2020 domin majalisa 9 ta amince da shi.

Idan majalisa ta amince da kudirin, hakan zai bawa gwamnatin tarayya (FG) ikon mallakar duk wasu albarkatun cikin ruwa; na zahiri da badini; a karkashin wata sabuwar hukuma da kudirin ke neman majalisa ta amince a kirkira.

Da ya ke mayar da martani a kan sake mayar da kudirin, Soyinka ya bukaci majalisa ta sake yin watsi da shi sannan ta sokeshi gaba daya.

Soyinka ya zargi Buhari da sauran shugabannin Najeriya na baya da rashin alkibla da hangen nesa da kuma gazawa wajen warware matsalolin Najeriya da suka hada da samar da ruwan sha.

"Kudirin da aka yi watsi da shi bayan jama'a sun bayyana fushinsu shekaru biyu da suka wuce, yanzu an sake dawo da shi ta bayan gida.

"Gwamnatin da ta gaza wajen warware matsalolin jama'arta, amma ga shi ta kafe wajen zartar da kudirin da zai zama dokar da za ta take hakki da 'yancin miliyoyin jama'a," a cewar wani bangare na jawabin Soyinka.

Farfesa Wole Soyinka ya caccaki shugaba Buhari a kan shirin kirkirar wata sabuwar doka a Najeriya
Farfesa Wole Soyinka da Buhari
Asali: UGC

"Fadar shugaban kasa, Aso Rock, na son mallaka tare da kwace dukkan iko da albarkatun cikin ruwa a kaf fadin ruwan da ke Najeriya, hakan ya hada da albarkatun zahiri da na badini da ke ciki ko karkashin kowanne ruwa da ke Najeriya.

DUBA WANNAN: Kaso 40 na maza ma su aure suna neman maza 'yan uwansu - Jaruma Halima Abubakar

"Ruwa, wanda ya kasance wata dukiya ta dukkan bil'adama, yanzu wata gwamnati tana son kwace iko da shi.

"Gwamnati ta gaza wajen samar da ruwa domin amfanin jama'a irinsu sha da girki, amma yanzu ta na shirin karbe iko da ruwan da ke manyan koramu da teku da wanda ke kwarara, zasu yi amfani da gwamnati wajen rabasu ga wadanda suke so.

"Bayan hakan kuma me zasu hara nan gaba? watakila ruwan sama, babu wanda ya sani. Na soki kudirin, na sake sukar dawo da shi kuma lokaci ya yi da ya kamata mu tashi domin daukan mataki a kan sake dawo da shi yanzu da nan gaba," a cewar Soyinka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel