Bunkasa rayuwa: Gwamnatin Buhari ta fitar da N10bn don tallafawa direbobi

Bunkasa rayuwa: Gwamnatin Buhari ta fitar da N10bn don tallafawa direbobi

- Gwamnatin Tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta amince da fitar da N10bn a matsayin tallafi ga direbobi

- A cewar ma'aikatar zirga zirga ta kasa, bayar da tallafin zai taimaka wajen rage wahalhalun da direbobin ke fuskanta a dalilin annobar COVID-19

- Ministar tana kan tattaunawa da ma'aikatar ayyuka da gidaje dangane da hanyoyin da za a bi don samun kudaden shiga ta fuskar zirga zirga

Gwamnatin Tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta amince da fitar da N10bn a matsayin tallafi ga direbobi da kungiyoyin da ke kula da su.

A cewar ministar zirga zirga na cikin gida, Sanata Gbemisola Saraki, tallafin zai taimaka wajen rage wahalhalun da direbobin ke fuskanta a dalilin annobar COVID-19.

Ta yi nuni da cewa yanzu haka kudaden na a hannun ma'aikatar masana'antu da kasuwanci, tana mai cewa ma'aikatar ta na kan shirye shiryen rabon kudaden.

Ministar ta bayyana hakan ne a ziyarar da shugaban kungiyar direbobi ta kasa (PTONA), Engr. Isaac Uhunwagbo ya kai mata tare da kwamitin amintattu na kungiyar a Abuja.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan watsa labaran ministar, Eric Ojiekwe.

KARANTA WANNAN: Don girman Allah a dakatar da shirin BBNaija - Malamin coci ya roki FG

Bunkasa rayuwa: Gwamnatin Buhari ta fitar da N10bn don tallafawa direbobi
Bunkasa rayuwa: Gwamnatin Buhari ta fitar da N10bn don tallafawa direbobi
Source: Twitter

Saraki, yayin da take cewa kaso 90 na 'yan Nigeria na tafiye tafiye ne a tituna, ta ce gwamnatin tarayya za ta samar da wani tsari da zai bunkasa fannin.

A dangane da matsalolin da direbobi ke fuskanta daga gwamnatin jihohi da masu ruwa da tsaki, ta bada tabbacin cewa za ta tattauna matsalar da kungiyar kwamishinonin zirga zirga ta kasa.

Ministar ta kuma bayyana cewa tana kan tattaunawa da ma'aikatar ayyuka da gidaje dangane da hanyoyin da za a bi don samun kudaden shiga ta fuskar zirga zirga.

Ta kara da bukatar su da su kaucewa duk wasu laifuka da kuma gudanar da ayyukansu bisa doka da oda, tare da hadin guiwa da ma'aikatar da sauran hukumomin da abun ya shafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel