Gwamna Masari ya kaddamar da babban kamfani a jihar Katsina
- Gwamna Aminu Masari ya kaddamar da babban kamfanin tonon ma'adanai a jihar Katsina
- Masari ya ce an bude kamfanin ne don samar da ayyukan yi ga matasan jihar da kuma bunkasa fannin tonon ma'adan kasa
- Alhaji Salisu Mamman, shine shugaban hukumar gudanarwar kamfanin
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bude wani kamfanin hako ma'adanai mallakin jihar. Ya bude kamfanin ne tare da kaddamar da hukumar gudanarwarsa.
Masari wanda ya kaddamar da kamfanin a ranar Laraba a Katsina ya ce an bude kamfanin ne don samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin APC a jihar mai ci a yanzu ta dukufa ainun wajen samar da walwala da tsaron rayukan al'ummar jihar.
Ya ce fannin ma'adanan kasa na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin jihar, wajen samun kudaden shiga, musamman a yanzu da ake fuskantar karyewar tattalin arziki.
Gwamna Aminu Masari ya bayyana dalilin samar da kamfani mallakin jihar domin bunkasa nema da tonon ma'adanan da suke a cikin jihar.
KARANTA WANNAN: A gaban kotu, malamin coci ya amsa laifinsa na yiwa 'yan gida daya ciki

Asali: UGC
Masari ya bayyana cewa kamfanin an bude shi ne bisa hadin guiwa da hukumomin gwamnatin tarayya, da ke fafutukar tattali da alkinta ma'adanan kasa.
Gwamnan jihar ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta mayar da fannin ma'adanai ya zama fanni mai muhimmanci, wanda jihar ke son bunkasawa.
Ya ce Allah ya albarkaci jihar Katsina da kalolin ma'adanan kasa guda 37 a kananan hukumomi 34 na jihar.
A cewarsa, ire iren wadannan ma'adanai sun hada da gwal, Manganese, Kaolin, asbestos, iron ore, copper da Emerald, da dai sauransu.
Alhaji Salisu Mamman, shine shugaban hukumar gudanarwar kamfanin, kuma shugaban kamfanin Continental computer da kuma mambobin hukumar gudanarwa.
Sauran mambobin hukumar gudanarwar sun hada da, Alhaji Abba Yusuf, Alhaji Abdulkadir Aliyu Faskari, Alhaji Kabir Musa Kaita da kuma Yahaya Iro Dansani.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng