A gaban kotu: Malamin coci ya amsa laifinsa na yiwa 'yan gida daya ciki

A gaban kotu: Malamin coci ya amsa laifinsa na yiwa 'yan gida daya ciki

- Wani malamin coci mai shekaru 48, Nduka Anyanwu, ya amsa laifinsa na yiwa 'yan gida daya fyade har suka yi ciki

- ASP Roman Unuigbe, ya shaidawa kotu cewa wanda ake karar ya aikata laifukan ne a cikin watan Yuni, a yankin Oshodi, garin Lagos

- Sashe na 137 na laifukan Lagos, ya ce a yanke hukuncin daurin rai da rai ga wanda ya aikata laifukan lalata ga kananun yara

Wani malamin coci mai shekaru 48, Nduka Anyanwu, a ranar Laraba, ya amsa laifinsa na yiwa 'yan gida daya fyade har suka yi ciki.

Malamin cocin ya amsa laifinsa ne a gaban babbar kotun majistire da ke Yaba, jihar Lagos.

Anyanwu na fuskantar tuhuma kan aikata laifuka biyu duka akan fyade.

Biyo bayan amsa laifinsa akan laifukan da ake tuhumarsa, mai sharia'a Mrs. A. Adedayo, ta bayar da ajiyarsa a gidan gyara hali, inda ta daga shari'ar zuwa ranar 15 ga watan Satumba.

Tun farko, jami'i mai shigar da kara, ASP Roman Unuigbe, ya shaidawa kotun cewa wanda ake karar ya aikata laifukan ne a cikin watan Yuni, a yankin Oshodi, garin Lagos.

KARANTA WANNAN: Dalilai 4 da suka sa Lionel Messi zai bar Barcelona

A gaban kotu: Malamin coci ya amsa laifinsa na yiwa 'yan gida daya ciki
A gaban kotu: Malamin coci ya amsa laifinsa na yiwa 'yan gida daya ciki
Asali: Facebook

Ya ce wanda ake zargin, ya kasance malamin coci, ya yiwa yaran biyu fyade, suna da shekaru 17 da sha 13, (sai dai an boye sunayensu), a lokuta daban daban, har suka dauki ciki.

A cewarsa, wanda ake zargin ya yi lalata da yan gida dayan ne a cikin cocinsa, da sunan yana yi masu addu'a ta musamman.

Unuigbe ya kara da cewa laifin da Anyanwu ya aikata ya sabawa doka ta 137 da ke cikin kundin laifuka na jihar Lagos, 2015.

Sashe na 137 na nuni da cewa, za a yanke hukuncin daurin rai da rai ga wanda ya aikata laifukan lalata ga kananun yara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel