Dalilai 4 da suka sa Lionel Messi zai bar Barcelona

Dalilai 4 da suka sa Lionel Messi zai bar Barcelona

Linonel Messi, wanda ake ikirarin kasancewar dan kwallo mafi daraja a duniya, a ranar Talata ya sanar da bukatar ficewarsa daga kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona, lamarin da ya girgiza duniyar wasanni.

Da yawa na kallon Messi a matsayin mutum mai son zama a kulob daya, sai dai yanzu kwatsam ya ce yana son barin Barcelona, lamarin da ya girgiza duniyar wasanni.

Da yawa na mamakin yadda Messi ya yanke wannan hukunci na barin kulob din da kuma birnin da ake ganin ya dauke sa kamar gidansa.

A ranar Talata, komai ya canja. Messi, mafi dadewar dan wasa a Barcelona, ya bukaci barin kungiyar kwallon kafar.

Ga wasu dalilai hudu da su ka sa Messi zai bar Barcelona:

  • Gaza dawo da Neymar kungiyar Barcelona:

Kafin fara kakar wasanni ta 2019/2020 da aka kammala yanzu, Messi ya bukaci a dawo da Neymar, dan asalin kasar Brazil, wanda ya bar kungiyar a 2017 zuwa kungiyar PSG.

Messi na da kyakkyawar alaka tsakaninsa da Neymar wacce ta zarce ta taka leda. Tare da Suarez, 'yan wasan uku suka zamo abun tsoro, har suka ci kofin 2015.

KARANTA WANNAN: Sakamakon rikicin makiyaya da manoma a Nigeria, anyi asarar akalla $12b

Dalilai 4 da suka sa Lionel Messi zai bar Barcelona
Dalilai 4 da suka sa Lionel Messi zai bar Barcelona
Asali: Twitter

Messi ya dauki Neyamar a matsayin magajinsa kuma a yanzu da shekaru ke ja, yana son wanda zai rinka taimaka masa. Sai dai shuwagabannin Barcelona sun gaza dawo da Neyamar.

A karshe ma dai sai kungiyar ta sayo Griezmman, wanda kuma tasu bata zo daya da Messi ba.

  • Sayen 'yan wasan da basu da amfani:

Messi ya jima yana takaicin yadda kungiyar ke sayo 'yan wasan da basu da amfani. Tun daga Dembele zuwa Griezmman, Martin Braithwaite da Paulinho, Messi na kallon taron tsintsiya ne ba shara.

Wannan dalilin ya sa ya zamo kamar shi kadai ne ke buga wasan a fili.

  • Wulakanta Suarez:

Sabon kocin kungiyar, Ronald Koeman ya sanar da abokin Messi, Luis Suarez a ranar Litinin cewa ba ya bukatarsa a kakan wasa mai zuwa. Suarez, ya kadu da ya samu labarin.

Hakan ya batawa Messi rai. Ya na ganin ba hakan bane ya dace a sakawa mutum na uku mafi tsada a tarihin kungiyar. Zai bar kungiyar ne don kwatarwa Suarez 'yancin sa.

  • Dawowa daga rakiyar hukumar gudanarwar kungiyar:

Ran Messi ya baci game da yadda hukumar gudanarwar kungiyar, bisa shugabancin Josep Barmoteu ta ke kula da 'yan wasa. A zuwan COVID-19, an ragewa 'yan wasan albashi zuwa kashi 70.

Sai dai biyan albashin ya zama ala kai kai, wanda har ya sa 'yan wasan suka fara dawowa daga rakiyar hukumar gudanarwar kungiyar.

Labarai da yawa na ci gaba da yawo a kafofin watsa labarai musamman na kasar Barcelona. Da wadannan dalilai ake ganin Messi ya yanke shawarar barin kungiyar kwata kwata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel