Dr. Obadiah Mailafia ya yi murabus daga NIPPS, ya fadi dalili

Dr. Obadiah Mailafia ya yi murabus daga NIPPS, ya fadi dalili

- Dr. Obadiah Mailafia, ya yi murabus daga mukaminsa a cibiyar koyar da tsare tsare ta NIPPS

- Mailafia ya ce ya jiye aikin ne a kashin kansa, da kuma nuna fushinsa kan kashe kashen Kudancin Kaduna

- Idan za a iya tunawa, hukumar tsaro ta SSS, ta tuhumi Mr Mailafiya kan zargin wani gwamnan Arewa da zama shugaban Boko Haram

Tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Nigeria, CBN, Dr. Obadiah Mailafia, ya yi murabus daga mukaminsa a cibiyar koyar da tsare tsare ta NIPPS.

An ruwaito cewa Mr Mailafia ya kasance shugaba a NIPSS, cibiyar koyon bincike da tsare tsare ga ma'aikatan gwamnati, shuwagabanni masu zaman kansu.

Cibiyar na a garin Kuru, jihar Filato.

Da ya ke fadin dalilin murabus dinsa, Mr Mailafia ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa ya ajiye aikin ne a kashin kansa, da kuma nuna fushinsa kan kashe kashen Kudancin Kaduna.

Ya ce: "Babu wanda ya matsa mun ko ya umurce ni na ajiye aikin. Nine na ajiye a kashin kaina.

"Ni na yanke shawarar barin aikin, a iya tunanina, idan har ana ci gaba da kashe jama'ata, sannan ana nuna kabilanci ga jama'ata, to ba zan iya yin shiru ba.

KARANTA WANNAN: An kashe kasurgumin makashin mutane da ya addabi jihar Ogun

Dr. Obadiah Mailafia ya yi murabus daga NIPPS, ya fadi dalili
Dr. Obadiah Mailafia ya yi murabus daga NIPPS, ya fadi dalili
Asali: UGC

"Wannan shine dalili, kuma hukumar gudanarwar cibiyar ta karbi takardar murabus dina.

"Na basu wa'adin kwanaki 30 daga ranar 18 ga watan Agusta zuwa 18 ga watan Agusta lokacin da murabus din zai yi aiki. Kuma murabus dina shine mafi a'ala ga kowa," a cewarsa.

Idan za a iya tunawa, hukumar tsaro ta SSS, ta tuhumi Mr Mailafiya biyo bayan wata hira da yayi da gidan rediyo a Lagos, inda ya zargi wani gwamnan Arewa da zama shugaban Boko Haram.

A baya bayan nan, wata kungiya mai da'awar wanzar da zaman lafiya, CCPSNN, ta yi kira ga hukumar gudanarwar cibiyar NIPSS da ta kori Malami akan kalamansa ga gwamnan.

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta, shugaban kungiyar Sali Usman da Sakatarensa Kefas Ndang, sun ce Mailafia bai cancanci aikin gwamnati ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel