Yanzu-yanzu: An kashe kasurgumin makashin mutane da ya addabi jihar Ogun

Yanzu-yanzu: An kashe kasurgumin makashin mutane da ya addabi jihar Ogun

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu na nuni da cewa Rundunar 'yan sandan jihar Ogun sun samu nasarar kashe kasurgumin makashin mutane da ya addabi jihar, mai suna Feyisola Dosunmu, mai shekaru 28.

Babban makashin wanda aka fi saninsa da 'Spartan', an gano mabuyarsa ne a wani yanki na Iperu a jihar, inda kuma 'yan sanda suka samu nasarar kashe shi.

TVC News ta ruwaito cewa jami'in hulda da rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 25 ga watan Agusta.

A wani labarin, gwamnan jihar Dapo Abiodun ya magantu kan kisan, yana mai cewa: "Wannan shine karshen sa (Feyisola Dosunmu da aka fi sani da Spartan)."

KARANTA WANNAN: Ya dawo daga banki, 'yan fashi sun kashe shi sunyi awon gaba da kudin

Yanzu-yanzu: An kashe kasurgumin makashin mutane da ya addabi jihar Ogun
Yanzu-yanzu: An kashe kasurgumin makashin mutane da ya addabi jihar Ogun
Asali: UGC

A wani labarin kuwa; Rundunar 'yan sanda a ranar Talata ta ce 'yan fashi sun kashe wani mutumi a ranar Litinin kusa da gidan gwamnatin jihar da ke Ibadan, bayan fitowa daga banki.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mutumin mai suna Taoreed Alao, ya gamu da ajalinsa ne a kan titin sakatariya da ke Agodi, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

An kashe shi ne da misalin karfe 1:30 na rana bayan da 'yan fashin suka bibiyeshi tun daga bankin da yafito, suka tsayar da shi tare da harbeshi a kan mashin dinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa mamacin ya cire N150,000 da kuma N296,000 daga wani banki a yankin Bodija, birnin Ibadan.

Jami'in hulda da rundunar 'yan sanda na jihar, Olugbenga Fadeyi, wanda ya tabbatar da faruwar kisan ya ce, an garzaya da Mr Alao asibitin jihar Adeoyo, inda a nan ya bar duniyar.

Ya kara da cewa an ajiye gawar mamacin a cikin asibitin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel